Faifan bidiyon mata 14 da Boko Haram ta kama ya ta da kura
A ranar 20 ga Yuni ne wadansu ’yan bindiga da ake zargi ’yan kungiyar Boko Haram suka kai wa jerin gwanon motocin da ke rakiyar wata gawa daga Maiduguri zuwa karamar Hukumar Askira/Uba a daidai kauyen Abare-Dalwa mai nisan kilomita 31 daga Maiduguri inda suka kashe wadansu mutane suka kuma sace wadansu matan aure 14, […]

A ranar 20 ga Yuni ne wadansu ’yan bindiga da ake zargi ’yan kungiyar Boko Haram suka kai wa jerin gwanon motocin da ke rakiyar wata gawa daga Maiduguri zuwa karamar Hukumar Askira/Uba a daidai kauyen Abare-Dalwa mai nisan kilomita 31 daga Maiduguri inda suka kashe wadansu mutane suka kuma sace wadansu matan aure 14, sai dai faifan bidiyon da ke nuna matan ya dada tado da bukatar al’ummar yankin na neman a ceto su.
Sace matan ya jefa tsoro da fargaba a zukatan ’yan uwansu, inda dattawan yankin suka nemi hukumomi su hanzarta ceto su.
Kakakin dattawan yankin, Barista Modu Bukar ya ce, “Matan 14 da aka sace suna rakiyar gawar wata ’yar sanda ce zuwa Askira/Uba amma sai wannan lamari ya rutsa da su. Lokacin da abin ya faru Shugaban riko na karamar Hukumar Askira/Uba ya sanar da ’yan sandan jihar domin daukar mataki na gaba amma har yanzu shiru muke ji kamar an shuka dusa. Muna rokon Gwamnatin Tarayya ta duba wannan
lamari da nufin ceto matan domin ’yan uwansu sun shiga cikin mummunan yanayi kuma yawancinsu ma’aikata ne da suke daukar nauyin mutane da yawa a gidajensu.”
Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Mista Damian Chukwu, ya nuna bakin ciki da damuwa game da aukuwar lamarin, ya c rundunar ba ta yi shiru ne ba akwai binciken da take yi don daukar matakan da suka dace, domin idan jami’an tsaro suna bincike ba dole ne su fito fili su shaida wa kowa ba.
Wata kafar watsa labarai ta nuna matan 14 suna tabbatar da cewa an sace su ne kuma suna neman agaji daga hukumomi.