Faifan bidiyon Rabaren Mbaka kan Jonathan ya ja hankalin mutanen Legas

Wani faifan bidiyo da Rabaren Fada Ejike Mbaka ya fitar, inda ya yi kira ga Shugaba Jonathan ya sauka daga kan karagar mulki ya ja hankulan jama’a a jihar Legas.Rabaren Fada Ejike Mbaka, Shugaban Cocin Adoration Ministry da ke Jihar Inugu ya shafe tsawon fiye da awa daya yana caccakar salon mulkin Shugaban Jonathan a […]

Faifan bidiyon Rabaren Mbaka kan Jonathan ya ja hankalin mutanen Legas
Faifan bidiyon Rabaren Mbaka kan Jonathan ya ja hankalin mutanen Legas

Wani faifan bidiyo da Rabaren Fada Ejike Mbaka ya fitar, inda ya yi kira ga Shugaba Jonathan ya sauka daga kan karagar mulki ya ja hankulan jama’a a jihar Legas.
Rabaren Fada Ejike Mbaka, Shugaban Cocin Adoration Ministry da ke Jihar Inugu ya shafe tsawon fiye da awa daya yana caccakar salon mulkin Shugaban Jonathan a lokacin da yake gudanar da wa’azin karshen shekara ga membobinsa.
Ya ce shekarun da Shugaba Jonathan ya yi yana mulki bai tabuka komai ba, saboda haka abin da ya kama ce shi, shi ne, ya sauka ya bai wa Janar Buhari mulki.
Binciken Aminiya ya gano cewa jama’a sun yi ta tura wa ’yan uwa da abokan arziki faifan bidiyon don su kashe kwarkwatar idon.
Wadanda suka kalli faifan bidiyon, sun bayyana wa Aminiya cewa, sun yi mamaki maganganun da limamin cocin ya fada kan Jonathan.
Malam Jibrin Jibo ya bayyana cewa ‘gaskiya mun yi murna da farin ciki da muka ji, kuma muka gani kuru-kuru babban fasto ya fadi gaskiya ga Shugaba Jonathan. Idan da a ce dan Arewa ne ya yi wannan furuci da sai wasu su ce kiyayya ce don ba dan Arewa ba ne. To ga shi dan uwa, dan kudu kuma dan yankinsu da suka hada addini daya ya yi kira a gare shi da ya sauka daga kan mulki’.
Malam Sani shi ma cewa ya yi ‘Ni gaskiya ban yi mamaki ba, domin na san duk wanda ke son kasar nan da arziki, to ya kamata ya fito ya gaya wa shugaban kasa gaskiya, cewa, ba zai iya mulkin kasar nan ba, ya sauka daga kan mulki. Rabaren Mbaka ya burge ni, kuma ya yi abin da ya dace, tunda ya fada wa shugaban kasa gaskiya, zabi ya rage ga shugaban kasa’.
Rabaren Mbaka ya bayyana cewa duk abin da ya fada ba ra’ayinsa ba ne, kuma ya kamata Shugaba Jonathan ya dauki shawarar da ya ba shi da muhimmanci.
Ya bayyana ci gaban mulkin Shugaba Jonathan da bala’i ga ’yan Najeriya.
‘Goodluck Jonathan yanzu ya zama Badluck, wato rashin sa’a, ba zai iya mulkin kasar nan ba a da ina yabonsa, amma yanzu na gano cewa ba zai iya mulkin kasar nan ba. Mun shiga cikin halin tsaka mai wuya ba hanyoyi, babu tsaro, darajar Naira ta fadi; ba wuta, ba kayan more rayuwa. Shin za mu ci gaba da kasancewa cikin wannan halin kunci? Shin sun dawo da ’yan matan Chibok da aka sace?” Inji shi.