Falala da fa’idojin alwala ga Musulmi (2)

Da sunan Allah, Mai tausayi, Mai jinkai.  Dukkan yabo da godiya na Allah ne Ubangijin halittu.  Tsira da amincin Allah su tabbata ga mafificin bayinSa, Annabi Muhammadu dan Abdullahi Balarabe, tare da alayensa da sahabbansa, masu daraja. Bayan haka, yau tsokacin namu zai ci gaba ne daga:Wankin fuska:  Wannan aiki ne wanda yake tilas a […]

Falala da fa’idojin alwala ga Musulmi (2)
Falala da fa’idojin alwala ga Musulmi (2)

Da sunan Allah, Mai tausayi, Mai jinkai.  Dukkan yabo da godiya na Allah ne Ubangijin halittu.  Tsira da amincin Allah su tabbata ga mafificin bayinSa, Annabi Muhammadu dan Abdullahi Balarabe, tare da alayensa da sahabbansa, masu daraja.
Bayan haka, yau tsokacin namu zai ci gaba ne daga:
Wankin fuska:  Wannan aiki ne wanda yake tilas a kula da shi, a yi shi cikakke don yin biyayya ga abin da Manzo, (Sallallaahu Alaihi Wasallam), ya ce wajen kaiwa matuka ga cika alwala. Kodayake magana ce da ta hade tun daga farkon alwalar har karshenta.  Fuska ta hade filin da yake tsakanin kunnen dama da na hagu (a fadi) da kuma tsakanin mafitar gashi a goshi (da aka sani ta al’ada) zuwa karshen haba (a tsawo).  Duk wannan fili, tilas ne a hade gaba dayansa, a murza kowane lungu, na kwarin idanu da karkashin hanci da labba, kowane gefe a wanke shi sosai, a wankin farko.  Wannan kuwa haka yake, domin Manzon Allah, (Sallallaahu Alaihi Wasallam), ya yi alwala da wanki daidai.  Ya yi da wanki bibbiyu.  Ya yi da wanki uku-uku.  Saboda haka ashe kowane wanki za a yi, lallai ne na farko ya kasance gamamme, in ba haka ba kuwa, ko wanki nawa aka yi, matukar na farkon bai game ba, to a kansa ake dabawa, har sai lokacin da ya cika, sannan a nemi wanki na biyu da na uku.
Wannan babban al’amari ne da yake da bukatar a lura da shi sosai.  Yin hakan zai taimaki mutum ya rika jin cewa ya yi koyi da abin da shari’a ta ajiye, kuma zai fi sa ran samun kyakkyawan sakamako.  Da yawa mutane kan yi wanki fuskar mage ko ta yara kanana, ba tare da kulawa ba.  Lallai ne mai ibada ya rika kawo hankalinsa, ya kasance halarce, a kan abin da yake aiwatarwa, a duk yayin da yake gudanar da kowane irin aiki na ibada.
Wankin hannu:  Hannun da ake zance a kansa, a nan, shi ne abin da ya hade tun daga kan ’yan yatsu har zuwa karshen gwiwa. Na fara kawo wannan bayani ne saboda mafi yawan masu alwala, sukan dauka cewa abin da ke tsakanin wuyan hannu zuwa gwiwa ake wankewa – wai saboda an wanke ’yan yatsu zuwa wuyan hannu tun farkon alwala, kamar yadda da yawa wasu kan fadi, idan an yi musu tambihin ba su wanke wurin ba.  Daga wuyan hannu zuwa gwiwa, in babu samansa, sai a ce masa dungun hannu ke nan. Wannan shi ne babban kuskuren da mafi yawan masu alwala suke tafkawa – kuma za a iske mutane ne mabambanta a jinsi daban-daban a matsayi na kowane gefe, wato manya da kanana. Wani lokaci ma har da wadanda ake ganin masana al’amarin addini ne da kan karantar da littattafai manya da kanana, wadanda suka shafi hukunce-hukunce daban-daban wato masu ilimi.
Idan an debi ruwan, an kwararo shi a hannun, lallai ne a wanke shi ko’ina, tun daga kan yatsu zuwa gwiwar hannu, a murza a kewaya kowane gefe, a shigar da gwiwar hannun, a cudanya, a wanke ko a tsettsefe tsakanin ’yan yatsun nan.  Tsettsefe ’yan yatsun (hannu da kafa) tilas ne, sai dai idan a yayin da ake wanke hannun (ko kafar), an game ko’ina.  Hasali ma, a wani bayanin cewa aka yi sai a hade ’yan yatsun dama a goga samansu a cikin tafin hannun hagu, kamar yadda za a yi wa yatsun hannun hagun a cikin tafin hannun dama, saboda dai a tabbatar da an game ko’ina na hannun.  Kuma kamar yadda bayani ya gabata a wajen wankin fuska, lallai ne wannan wanki na farko ya game kowane gefe, ta yadda ko ba a kara na biyu ko na uku ba, shi ke nan alwala ta cika. To sannan sai a yi wanki na biyu da na ukun, kamar na farko.
Shafar kai: Maganar da ta fi karfi cikin al’amarin shafar kai ita ce a shafa shi dukansa.  Za a hada kan yatsun hannaye biyu a goshi, daidai matsirar gashi ta al’ada, alhali manyan yatsu suna gefen kunnuwa, sannan sai a gudanar da hannaye zuwa karshen keya a dawo, ta yadda zai kasance an shafe dukkan kai gaba dayansa, ta wannan sifa.  Daga nan kuma sai a sanya yatsun nune (dan-Ali) a cikin kunnuwa, a sanya manyan yatsu a karkashin kunnuwa ta baya, a gudanar da su zuwa gaba, alhalin an gudanar da yatsun ciki zuwa murza fatun kunnuwan, ta yadda hakan zai kasance an shafa ciki da wajen fatun kunnuwan – an yi shafar kunnuwa ke nan tare da ta kai, a lokaci guda. Wannan hanyar ma ita ta fi inganci.
Wanke kafa: Daga kan idanun sawu zuwa abin da ya je kasa shi ne filin kafa, kuma shi ne ake bukatar a wanke sosai. Bone ya tabbata ga karshen kafa (duga-dugai), saboda haka, lallai a yi hattara sosai wajen ganin an wanke kafafu sosai, musamman ma masu faso ko kauje ko kaushi. Ana sanya kananan yatsun hannu (khinsar) wajen tsettsefe yatsun kafa – kamar yadda aka nuna a zantukan da malaman Sunnah suka yaba da maganar haka din.
Wannan ita ce alwala cikakkiya, in Allah Ya so, kamar yadda ake bukata.  A nan gaba, za mu jero fa’idojin alwala, in Allah Ya so.  Muna fata Allah Ya yi mana muwafaka.
Littattafan da aka duba aka gudanar da wannan tsokaci sun hada da Sahihu fikhus sunnah wa adillatihi na Abu Malik Kamal bin Assayyid Salim da Taudhihul ahkam min bulughil maram na Abdullaahi bin Abdurrahman Albassam da Sifatis Salatin Nabiy da Samaruddaniy – sharhin Risaala da Fatawa Islamiyya (na Ingilishi) – da fatar samun dacewa daga Allah Madaukakin Sarki!!

Falala da fa’idojin alwala
A nan za mu gabatar da falala da fa’idojin alwala, kamar yadda Malam Abu Malik Kamalu bin Assayyid Salim, ya jero su a littafinsa Sahih Fikhussunnah wa adillatuh, in Allah Ya so.  Falala na iya daukar ma’anar fa’ida, kamar yadda ita ma fa’ida take iya daukar ma’anar falala. Ta kowane hali dai abin da ake so a nuna a nan shi ne wadansu amfanoni da akan samu a cikin yin alwala, koda kuwa ba za a yi Sallah da ita ba, kamar yadda za a gani.  
Sai mako na gaba, in Allah Ya kai mu!