Falalar Darare Goma na Zul-Hajji

Allah Madaukaki Ya ce: “Ina rantsuwa da Alfijir. Da Darare Goma.” (Alfajr:1-2). Malamai sun kai sun kawo kan wadanne ne Darare Goma. Kuma mafi rinjaye sun tafi a kan darare goma na farkon watan Zul Hajji ne, kamar yadda Ibnu Kasir ya ce: “Darare Goma: Ana nufin goman Zul Hajji ne kamar yadda Ibnu Abbas […]

Falalar Darare Goma na Zul-Hajji

Allah Madaukaki Ya ce: “Ina rantsuwa da Alfijir. Da Darare Goma.” (Alfajr:1-2). Malamai sun kai sun kawo kan wadanne ne Darare Goma. Kuma mafi rinjaye sun tafi a kan darare goma na farkon watan Zul Hajji ne, kamar yadda Ibnu Kasir ya ce: “Darare Goma: Ana nufin goman Zul Hajji ne kamar yadda Ibnu Abbas da Ibnu Zubair da Mujahid da malamai da dama na Salafus Salih da Khalafus Salih suka fadi.” (Tafsirul ku’anil Azim, mujalladi na 4 shafi na 539-540).

Ibnu Sa’adi (Rahimahllah) ya ce, “A bisa mafi ingancin magana su ne dararen goma na Ramadan ko darare goma na Zul Hajji. Su darare ne da suka kunshi ranaku masu falala, ayyukan ibada da neman kusanci ga Allah suna aukuwa a cikinsu fiye da wasunsu… A cikin darare goma na Zul Hajji ne ake tsayuwar Arfa wanda Allah Yake yin gafara ga bayinSa, gafarar da Shaidan ke bakin ciki da ita, domin Shaidan bai taba ganin kaskanci da tozarci irin na Ranar Arfa ba, saboda abin da yake gani na sassaukar Mala’iku da rahama daga Allah a kan bayinSa, kuma ayyukan Hajji da Umara na gudana a cikinsu. Wadannan abubuwa masu girma sun cancanci Allah Ya yi rantsuwa da su.” (Taisirul Karimir Rahman, mujalladi na 7 shafi na 621-622).

An karbo daga Ibnu Abbas (RA) daga Annabi (SAW) ya ce: “Babu ranakun da ayyuka nagari suka fi soyuwa a wurin Allah daga wadannan ranaku goma (na Zul-Hajji). (Sahabbai) Suk ce, Ya Rasulullahi! Ko da jihadi a tafarkin Allah? Ya ce, “Ko da jihadi a tafarkin Allah, sai dai in mutum ya fita da ransa da dukiyarsa bai dawo da komai daga cikinsu ba.” (Buhari). Ibnu Rajab ya ce: “Wannan Hadisi ya nuna aiki a cikin ranakunsa (Ranaku 10 na Zul-Hajji) ya fi soyuwa a wurin Allah daga aiki a sauran ranakun duniya ba tare da toge komai daga gare su ba. Kuma idan ya kasance mafi soyuwa ga Allah, to shi ne mafi falala a wurinSa.” (Lada’iful Ma’arif, shafi na 458).

Allah Madaukaki Ya ce: “Kuma ka yi yekuwa ga mutane game da Hajji su zo maka a kasa da kuma kowane abin hawa, su zo daga kowane sako mai nisa. Domin su halarci abubuwan amfani gare su, kuma su ambaci sunan Allah a ranaku sanannu bisa abin da Ya arzuta su na dabbobin ni’ima.” (Hajji: 27-28).

Ibnu Abbas ya ce: “Ranaku sanannu” su ne: “Ranakun nan goma.” (Buhari).

Ibnu Rajab ya ce: “Jamhurun Malamai sun tafi a kan ranaku sanannu su ne, goma na Zul-Hajji, daga cikinsu akwai Ibnu Umar da Ibnu Abbas da Alhasan da Adda’u da Mujahid da Ikramata da kattada da Nakha’i, kuma shi ne maganar Abu Hanifa da Shafi’i da Ahmad a mafi shaharar abin da aka samu daga gare shi.” (Lada’iful Ma’arif, shafi na 471).

Ayyukan da ake son yi a cikinsu:

Ana son yawaita kabbarori da tahlili da tahamidi a cikinsu. Domin bayan Annabi ya fadi Hadisin da muka kawo a baya sai ya ce: “Ku yawaita tahlili (fadin La’ilaha illallah) da takbiri (Allahu Akbar) da tahmidi a cikinsu.” (Ahmad da Baihaki suka ruwaito).  

Kuma an so a yi kokari wajen aikata sauran ayyukan da’a a cikin ranaku da dararen. Yazid bin Abu Zayyad ya ce: “Na ga Sa’idu bin Jubair (Rahimahullah) da Abdurrahman bin Abu Laila da Mujahid ko biyu daga cikin wadannan uku na daga wadanda muka gani daga fakihan mutane suna yawaita fadin, Allahu Akbar! Allahu Akbar! La’ilaha illallah wallahu Akbar, Allahu Akbar, wa lillahil hamdu a cikinsu (ranaku goma na Zul-Hajji).” (Ahkamul Idaini na Faryani, shafi na 119).

Yawaita sauran ayyukan da’a:

Sa’idu bin Jubairu ya kasance idan goman suka shigo yana kokarin sosai wajen ayyukan da’a, har an ruwaito shi yana cewa: “Kada ku kashe fitilunku a darare goma (kinaya a kan a yi ta karatun kur’ani da nafilfili).” (Alhilyatul Auliya, Mujalladi na Mujalladi na 4 shafi na 281).

A cikin wadannan kwanaki goma ne ake samun Ranar Arfa, wadda ta tara falaloli da dama da suka hada da yawan ’yanta bayi daga wuta da Allah zai yi da alfahari da Allah zai yi ga mala’ikunSa kan yawan mahajjata.

Sannan a Ranar Arfa ce Allah Madaukaki Ya cika tare da kammala addininSa ga al’umma kuma Ya cika ni’imarSa a kanta.  Har ma wani Bayahude ya ce da Amirul Muminina Umar bin Khaddabi (Allah Ya kara yarda a gare shi) da ga su Yahudawa aka saukar da ayar kammala cikar addini da sun dauki wannan rana a matsayin Ranar Idi.

Saboda haka ana son yin azumi a ranar Arfa da addu’o’i. 

Malamai sun hadu cewa ta kowane hali a ranakun Idi biyu a hana yin azumi, koda na bakance ko kaffara kamar yadda Annawawi ya nakalto a sharhinsa ga Sahihu Muslim. (8/15). Kuma sun ce, hikimar hanin ita ce idan aka yi azumin kamar an ki amincewa da liyafar da Allah Ya shirya ga bayinSa ne. (Nilul Audar, 4/262).

Sunnah ce, a yi wanka a sanya sababbin kaya ko a wanke wanda suka fi kyau cikin tufafin a sa turare a fita masallacin Idi, maza da mata manya da yara tare da tsare ladubban fitar, wato kada mata sun caba ado ko sun sanya turare kuma kada a samu cakuduwar maza da mata da sauran abubuwan da shari’a ta hana.

Sunnah ce a rika fadin: “Allahu Akbar! Allahu Akbar!! La’ilaha illallah, Wallahu Akbar! Allahu Akbar! Walillahil hamdu.” Wadannan  kalmomi ana fata duk wanda Allah Ya raya zuwa ranar Idi ya rika maimaita su daga lokacin da ya fito zuwa Masallacin Idi da kuma duk lokacin da ya idar da Sallah ta farilla na tsawon yini uku. 

Idan aka dawo gida sai a yi yanka, an so mai Layya kada ya ci komai, sai ya yanka layyarsa ya yanki namanta musamman hanta ya fara da shi a wannan rana.

Ranar Sallah ranar ce ta murna da farin ciki da bukukuwa, to, sai dai kada wajen murna a wuce gona da iri. Kada murna ta sa a koma ga sabo. Kada murna ta sa a aikata bidi’o’in da za su bata kyawawan ayyuka.

Ladubban ranar Sallah:

1. Taya juna murna da duk lafazin da ya sauwaka, kamar “Allah Ya karba mana” da sauransu. An ruwaito cewa wadansu daga magabatan kwarai suna aikata haka. Misali Jubairu bin Nufair ya ce, “Sahabban Annabi (SAW) idan suka hadu da juna sukan ce, “Allah Ya karba mana, Ya karba muku.” Imam Ahmad ya ce Isnadinsa mai kyau ne, sannan Hafiz ya kyautata Isnadinsa a cikin Fathul Bari (2/517). A duba Tamamul Minnah na Albani don karin bayani. Kuma an ruwaito Imam Ahmad yana cewa: “Ba zan fara fada wa mutum haka ba, amma idan ya fada min zan amsa masa.” 

2.  Ziyartar ’yan uwa da makusanta da sada zumunta. Wannan mustahabbi ne a kowane lokaci, amma an fi karfafa shi a irin wannan lokaci, musamman ziyartar iyaye, domin ana sanya musu farin ciki, kuma haka cikar umarnin Allah ne na a kyautata musu.

3. Wadata abinci da abin sha: Babu laifi a wadata abinci da abin sha a wadannan ranaku ba tare da almubzzaranci ba, saboda fadinsa (SAW): “Ranakun Tashrik, ranaku ne na ci da sha da ambaton Allah.” Kuma ya halatta a yi wasannin da suke halal, saboda Hadisin Anas a wurin Abu Dauda da Nisa’i bisa Isnadi ingantacce da ya ce: “Lokacin da Annabi (SAW) ya isa Madina, ya iske su suna taruwa rana idoji, sai ya ce, “Kuna da wuni biyu da kuke wasanni a cikinsu, to, hakika Allah Ya musanya muku da mafiya alheri: “Ranar karamar Sallah da Ranar Layya.” 

Kuma ya halatta a yi wake-waken da suka halatta, saboda Hadisin A’isha (RA) cewa, “Manzon Allah (SAW) ya shiga wurina ina tare da wasu kuyangi biyu suna kida da waka (wasu sun ce da shantu) sai ya kishingida a kan tabarma ya juya fuskarsa. Sai Abubakar ya shigo ya yi min fada ya ce “Shaidan a gidan Annabi (SAW)? Sai Manzon Allah (SAW) ya kalle shi ya ce “kyale su- a wata ruwayar ya ce “Ya Abubakar ko wadanne mutane suna da Idi, wannan Idinmu ne.”