Falalar Hajji da goman farko na watan Zul -Hajji

Daga Hudubar Sheikh Aliyu bin Abdurrahman AlhuzaifiMasallacin Annabi, Madina Huduba ta Biyu:Hamdala da shahada da salati.Bayan haka ku bi Allah da takawa ya ku Musulmi! Domin takawa ita ce mafi alherin guzuri domin Ranar Hisabi da ita Allah Yake kyautata al’amuran bayi. “Duk wanda ya yi takawa ga Allah, Zai sanya masa sauki a cikin […]

Falalar Hajji da goman farko na watan Zul -Hajji

KA’ABA Mai alfarmaDaga Hudubar Sheikh Aliyu bin Abdurrahman Alhuzaifi
Masallacin Annabi, Madina

Huduba ta Biyu:
Hamdala da shahada da salati.
Bayan haka ku bi Allah da takawa ya ku Musulmi! Domin takawa ita ce mafi alherin guzuri domin Ranar Hisabi da ita Allah Yake kyautata al’amuran bayi. “Duk wanda ya yi takawa ga Allah, Zai sanya masa sauki a cikin al’amuransa.” (dalaki:4).
Ku sani ya bayin Allah! Lallai ibada hakki ne na Ubangijin talikai a kan mukallafai, kuma farilla ne da aka yi wa hatimi a kan mutane da aljanu. Allah Madaukaki Ya ce: “Kuma ban halicci aljanu da mutane ba face domin su bauta Min.” (Az-Zariyati:56).
Ibada ita ce mafi daukakar abin da Allah Ya karrama bayinSa da shi. Kuma da ita yake daukaka masu takawa. Da ibada zukata suke yin haske, zukata su tarbiyyantu, dabi’u su daidaita, hankula su kyautata, ayyuka su tsarkaka, rayuwa ta karu da kyautata da kyautatawa, Allah Madaukaki Ya yarda da bawa, kuma a samu daukaka a cikin Aljanna, a kankakre zunubai a ninninka kyawawan ayyuka.
Daga cikin rahamar Allah gare mu akwai aiko mana da mafi alaherin halitta Annabi Muhammad (SAW), yana mai bayyana mana abin da Ubangijinmu Ya yarda da shi gare mu na daga maganganu da ayyuka da kudurce-kudurce, yana yi mana gargadi daga abin da zai fusata Ubangijinmu na maganganu da ayyuka da kudurce-kudurce. Allah Madaukaki Ya ce: “Kamar yadda Muka aiko a cikinku wani Manzo daga cikinku, yana karanta ayoyyinMu a kanku. kuma yana sanar da ku Littafi da Hikima kuma yana sanar da kun abin da kuka kasance ba ku sani ba. Kuma ku tuna Ni, Ni kuma in tuna ku, ku gode Min kada ku butulce Min.” (Bakara: 151-152).
Ba domin Allah Ya aiko da Manzanni kuma Ya saukar da Littattfai tare da su ba, da dan Adam ya fi dabba bacewa, amma sai Allah Ya yi rahama ga mutane, Ya shar’anta addini Ya yi komai daki-daki, Ya daidaita alamun shiriya, masu rabo suka shiryu, shakiyyai suka kauce wa bayananSa.
Daga cikin rahamar Allah da hikimarSa da cikar iliminSa, sai Ya shar’anta ibada domin gyara zuciyar dan Adam, Ya shar’anta ibadoji iri-iri; Sallah da Zakkah da Azumi da Hajji da sauransu, domin tabbatar da cikar tarbiyyar  mutum da tsarkake shi ta kowace fuska. Allah Madaukaki Ya ce: “Allah ba Ya nufin Ya sanya wani kunci a gare ku, sai dai Yana nufin Ya tsarkake ku ne kuma Ya cika ni’imarSa a kanku, dammaninku kuna godewa.” (Al-Ma’ida: 6).
Hajji rukuni ne daga cikin rukunan Musulunci, kuma Allah Ya tara dukkan ayyukan ibada na zuciya da ikhlasi, kuma Ya tara ibada ta dukiya da magana da ta gabbai a cikinsa. Zamanin Hajji ya kunshi kalmar shahada mafi girman rukunin Musulunci. Ya tara Sallah da ciyar da dukiya da azumi ga wanda bai samu hadaya ba da umarni da alheri da hana munkari da hakuri da hadiye fushi da tausayawa da jin kai da sanin alheri da yakar zuciya da sauran ayyukan da Allah Ya farlanta. Kuma ya kunshi guje wa haramtattun ayyuka. Hajji aya ce daga ayoyin Allah masu girma da ke nuna cewa abin da Annabi Muhammad (SAW) ya zo da shi shi ne addinin gaskiya. Babu wata hukuma ko gwamnati ko wani karfi a duniya da zai iya tara mahajjata kowace shekara daga sassan duniya daga dukkan nau’o’in mutane masu mabambantan matsayi da jinsi su zo da zuciya cikie da shauki da soyayya suna masu mance wahalar doguwar tafiya da suka sha, suna masu farin ciki da barin kasashe da iyalai da abokansu, suna ji a jikinsu cewa lokacin aikin Hajji shi ne lokaci mafi sa’ada a rayuwa, suna girmama ayyukan Hajji suna ciyar da dukiya domin Hajji cikin jin dadi. Babu mai iya haka sai Allah Wanda sunanSa ya daukaka, siffofinSa suka girmama. Shi ne Ya ce wa BadadayyinSa Ibrahim (AS): “Ka yi kira a cikin mutane su zo maka a kafafu da duk wani mai daukar kaya, su zo daga kowane lungu mai nesa. Domin su halarci wasu abubuwan amfani gare su, kuma su ambaci Allah a wasu ranaku sanannu kana bin da aka azurta sun a daga dabbobin ni’ima. Ku ci daga gare su, kuma ku ciyar da mayunwanci fakiri.” (Hajji: 27-28).
Ibnu Jarir da Ibnu Kasir da wasu masu tafsiri sun cirato daga Ibnu Abbas (RA) cewa, lokacin da Allah Ya umarci Annabi Ibrahim (AS) ya yi kira ga mutane su zo aikin Hajji ya ce: “Ya Ubangiji! Yaya zan isa ga mutane alhali sautina ba zai je gare su? Sai (Allah) Ya ce: “Ka yi kira isarwa yana kanmu. Sai ya tashi tsaye a inda yake. Wasu suka ce a kan dutse wasu suka ce a dutsen Safa, wasu suka ce a Abu kubais. Ya ce: “Ya ku mutane! Lallai Ubangijinku Ya riki gida ku yi hajjinsa. Sai aka ce: Lallai duwatsu sun sunkuya (sun dauki) sautin ya isa dukkan sassan kasa har wanda ke cikin mahaifa da tsatso. Kuma kowane abu da ya ji na daga dutse da marmara da itatuwa suka amsa masa: Laibaikal lahumma labaika. Allah Ya rubuta wanda zai yi Hajji har zuwa Ranar kiyama.”
An so ga mahajjaci da wanda bai yi su yi gaggawar zuwaga kowane alheri da aiki nagari da na da’a a goman farko na watan Zul-Hajji. An karbo daga Ibnu Abbas (RA) ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce: “Babu wasu ranaku da aiki nagari ya fi soyuwa ga Allah kamar wadannan ranaku, (yana nufin goman farko)” Suka ce: “Ya Manzon Allah! Koda jihadi a tafarkin Allah?” Ya ce: “Koda jihadi a tafarkin Allah, sai dai in mutum ya fita da ransa da dukiyarsa bai dawo da komai daga cikinsu ba.” Buhari ya ruwaito.
Domin haka ana son yawaita ambaton Allah a cikin masallatai da hanyoyi da wuraren taro da kasuwanni da yayin da mutum ya kebanta shi kadai.
A cikin wadannan kwanaki goma ake samun Ranar Arfa. dan uwa Musulmi koda tsayuwar Arfa ta kubce maka, Allah Ya shar’anta maka azumtarta. An karbo daga Abu kattada (RA) ya ce: “An tambayi Manzon Allah (SAW) game da azumin Ranar Arfa sai ya ce: “Yana kankare zunubin shekarar da ta gabata da mai wadda ake ciki.” Muslin ya ruwaito. Kuma an karbo daga Ibnu Umar (RA) daga Annabi (SAW) lallai shi ya ce: “Babu wasu ranaku da suka fi girma a wurin Allah kuma aiki ya fi sonyuwa a gare shi a cikinsu daga wadannan ranaku goma. Don haka ku yawaita tasbihi da takbiri da tahamidi a cikinsu.” Ahmad ya ruwaito. Don haka ne Ibnu Umar da Abu Huraira suke fita kasuwa su rika kabbarori mutane suna koyi da su. Kamar yadda Buhari ya ruwaito.
Ku yi riko da ladubban Musulunci madaukaka da dabi’unsa kyawawa, ku tuba a wannan wata ku gyara ayyukanku ku ji tsoron abin da zai zo gaba. Ku yi nadama kan abin da ya gabata a rayuwarku. Ku gode wa Allah Madaukaki ku yi maSa shukura a bisa ni’imar zaman lafiya da imani da abubuwan da Yah ore muku na alherai da ibadoji. Ku gode maSa kan abin da Ya ba kuu na arziki da biyan bukatu da abin da Ya kare muku na daga ukubobi da cututtuka.    
Bayin Allah, “Lallai, Allah da mala’ikunSa suna salati ga Annabi. Ya ku wadanda suka yi imani! Ku yi salati a gare shi, kuma ku yi sallama domin amintarwa a gare shi.” (k:33:56).
Manzon Allah (SAW) ya ce: “Wanda ya yi salata a gare ni, Allah zai yi masa salati goma a madadinta.” Don haka ku yi salati a kan shugaban mutanen farko da na karshe, kuma shugaban manzanni. Ya Allah! Ka yi tsira ga Annabi Muhammad da iyalan Annabi Muhammad kamar yadda Ka yi salati a kan Annabi Ibrahim da iyalan Ibrahim, lallai Kai Abin godewa ne Mai girma. Ya Allah Ka kara aminci ga Annabi Muhammad da iyalan Annabi Muhammad kamar yadda Ka yi ga Annabi Ibrahim da iyalan Ibrahim. Lallai Kai ne Abin godewa Mai girma da aminci mai yawa. Ya Allah! Ka yarda da sahabban Annabika baki daya da tabi’ai da tabi’it tabi’ina da wadanda suka biyo su da kyautatawa har zuwa Ranar Sakamako, Ka hada da mu don rahamarKa ya Mafi rahamar masu rahama.