Falalar malamai: Ta’aziyyar masani Sheikh Ahmad Bamba (Qala Haddasana)
Allahu Akbar, shi mutum ne mai daraja a duniyar Musulunci saboda rikonsa ga Sunnah.
Sahabi Aliyu R.A ya fada ga Jabir dan Abdullahi R.A cewa “Duniya ta dogara ne akan abu hudu; Addini, da Malami, da mai yin aiki da ilimin sa sai Jahili wanda baya girman kai wajen neman sani, da kuma mawadaci wanda baya rowa da dukiyarsa.
Marigayi Sheikh Dokta Ahmad Bamba ya fada mana cewa ilimi ba komai bane sai sanin abu a zuciya da kuma gasgatarsa a zahiri, yayin da jahilci ke nuni da kiyaye abu a zuciya wanda a zahirance ba gaskiya bane. Saboda haka a cewarsa ba kawai rashin sanin abu ake kira jahilci ba, a’a har ma da sani gami da riko na abinda bai gasgata ba.
- El-Rufa’i ya umarci makarantun gwamnati a Kaduna su fara aiki sau 4 a sati
- Sai Buhari ya bar mulki za a ga amfaninsa — Bashir Ahmad
Rayuwa irin ta Dokta Ahmad madubi ce ga daukacin al’ummar Musulmi.
Shi mutum ne mai kyakkyawar fahimta ga lamurran addini, amma mai zafafawa wajen kare martaba irin ta Annabi Muhammad (S.A.W).
Mai kimanin shekaru 82 da haihuwa, wanda ya rasu a ranar Juma’a 7/1/2021, marigayi Dokta Ahmad Bamba ya shafe daukacin rayuwarsa wajen nema da kuma bayar da sani.
Ya shafe sama da shekara 20 yana daukar darasi a Madina, masallacin Annabi Muhammad S.A.W sannan ya fassara Littafin Muwadda, wallafar Imamuna Maliku Dan Anas daga harshen Larabci zuwa harshen Hausa, baya da karantarwarsa ga manyan littattafai irin su Sahihul Bukhari, Sahihu Muslim, Sunnani Darimi, da makamantansu duk a cikin harshen Hausa. Tabbas, rasuwarsa babbar asara ce ga kafatanin al’ummar musulmi musamman, Hausawa.
Ya zo a cikin littafin ‘Al-ilmu Huwal Imamu’ na Shekh Ibrahim Inyass cewa Hanyar aljanna tana hannun mutane guda hudu; malami, da mai gudun duniya da mai ibada da kuma mai jihadi fi sabilillahi. Shi malami idan ya kasance mai gaskiya ne cikin zuciyarsa, tabbas Allah zai azurta shi da hikima. Duk kuwa wanda aka baiwa hikima, alal hakika an bashi gagarumar baiwa anan duniya da gobe lahira kamar yadda yazo a cikin littafin Allah, Alkur’ani.
An tambayi Dan Mubarak cewa suwane ne mutane?, sai ya ce ‘Malamai’, sai aka ce masa su wanene sarakuna? sai ya ce masu gudun duniya, sai aka ce su wane ne kaskantattu?, sai ya ce masu cin duniya da addini. Don haka, ana iya cewa lallai malamai mutane ne masu daraja a cikin al’umma.
Abdul-Aswad yana cewa babu wani abu wanda ya fi Ilimi daukaka. Sarakuna masu yin hukunci ne ga jama’a, yayin da malamai ke yin hukunci a garesu.
Ahnaf R.A yana cewa malamai sun kusa kasancewa iyayen giji.. dukkan daukakar da ba a karfafeta da ilimi ba, karshen ta kaskanci ce.
Annabi Muhammad S.A.W ya fada cewa “Malamai, sune magada Annabawa” (Tirmizi, Abu Dawood da Ibn Maja duk sun ruwaito shi).
Allah Ta’ala kuwa ya fada cewa “Iyaka dai masu jin tsoron Allah sune Malamai” (Suratul Fathi, 28).
Babu bubatar zafafa yabo ga marigayi Mallam Ahmad Bamba, domin shi ba mai son yabo ko kwarzantawa bane a zamanin rayuwarsa, amma shi ne wanda ya jaddada Sunnah a kasar Hausa bayan da ta dauko disashewa, shi mutum ne wanda yake son Allah da Manzonsa, wanda yake tarbiyantar zukatan bayin Allah akan bautar Allah ta tsanin manzonsa Annabi Muhammad S.A.W da mayar da lamurra a gareshi, kuma mutum ne maras kwadayi, mai darajanta ilimi da darajanta kansa, gami da fadar gaskiya walau ga shuwagabanni ko ga mabiyansu.
Allahu Akbar, shi mutum ne mai daraja a duniyar Musulunci, tushen darajarsa kuwa bai wuce ga rikonsa ga Sunnar Annabi Muhammad S.A.W ba, da tsantsaininsa, kai ka ce shine Imam Maliku bn Anas ko Imam Hasanul Basri. Hakika, rayuwarsa ta kasance abar koyi ga al’ummar Musulmi.
Wani sashen masana sun fada cewa An fifita Imam Hasanul Basri akan sauran Tabi’ai, saboda abubuwa guda biyar;-
- Ba ya umarni da aikata wani aiki face ya fara aikatawa.
- Ba ya hanuwa ga barin wani aiki face ya fara hanuwa daga gareshi.
- Duk wanda ya nemi wani abu daga abinda Allah ya hore masa, zai bashi.
- Ya kasance yana wadatuwa da ilimin sa ga barin neman wani abu a wajen mutane.
- Ya kasance ciki da wajensa duk daya ne.
Tabbas, duk wadannan siffofi guda biyar sun tabbata ga Marigayi Sheikh Ahmad Ibrahim Bamba. Gashi kuma ya samu cikawa irin tasa. Da fatan Allah ya rahamshesu duka amin.
Abdullah bin ‘Amr Ibnul’Ash ya ruwaito daga Annabi Muhammad S.A.W cewa “Lalle, Allah baya dauke ilimi daga hanawarsa ga bayin sa. Sai dai yana dauke ilimi ne daga mutuwar malamai ta yadda tsarkakan mutane za su gushe, sai mutane su nada wawayen mutane a shugabanci. Sannan idan aka tambaye su, sai suyi magana ba da ilimi ba. Sai su tabe kuma su yi asara.” ( Al-Bukhari da Muslim suka ruwaito).
Kaicho da rashin babban masani Dokta Ahmad Bamba, to amma ya kamata kowa ya sani wannan duniya ba abar dauwama ba ce. Tabbas, kowanne mai rai zai dandana mutuwa. Kuma tabbas, yadda Dokta Ahmad ya koma ga mahaliccinsa, kowannen mu lokaci yake jira domin komawa zuwa ga Allah. Don haka ya kamata mu shagaltu wajen aiki da koyarwarsa, da neman ilimi, da bin Allah da kuma neman dacewar Allah da samun Aljanna.
Dafatan Allah Ya gafarta wa Dokta Ahmad Ibrahim Bamba, Allah Ya tallafi bayansa amin.