Falalar Ramadan: Wata na rahama, gafara, da tsira daga wuta

Ramadan wata ne mai cike da lada da alfarma, wanda ya kamata Musulmi su ribace shi yadda ya kamata.

Falalar Ramadan: Wata na rahama, gafara, da tsira daga wuta

Azumin watan Ramadan na daga cikin shika-shikan Musulunci, kuma Allah ne Ya wajabta shi a kan bayinsa.

Wannan wata yana da falala da lada mai yawa, domin Allah Ya keɓe shi da girma da ɗaukaka.

Ga wasu daga cikin falalar azumin watan Ramadan:

1. Ana buɗe kofofin Aljanna, ana rufe ƙofofin wuta, kuma ana ɗaure shaiɗanu. Wannan yana taimaka wa zuciyar Musulmi wajen yin alheri da kauce wa munanan ayyuka.

2. Yin azumi da tsayuwar sallar Tarawihi saboda Allah da neman lada, ana gafarta zunuban bawa da suka gabata.

3. Akwai daren Lailatul-Kadari, wanda ya fi wata dubu daraja. Duk wanda ya yi ibada a wannan dare yana mai imani da neman lada, za a gafarta masa zunubansa na baya.

4. Yin Umara a watan Ramadan yana daidai da yin aikin Hajji tare da Manzon Allah (SAW).

5. Watan Ramadan wata ne na Alƙur’ani, saboda a cikinsa aka saukar da shi. Don haka, ya dace a yawaita karanta shi.

6. Watan Ramadan wata ne na kyauta, ciyarwa da sadaka. Manzon Allah (SAW) ya fi yawan kyauta a wannan wata.

7. Baccin mai azumi ibada ne, domin yana rage sha’awa da kula da zuciya.

8. Mai azumi yana da farin ciki biyu:

  • Yayin da zai buɗe baki bayan azumi.
  • Lokacin da zai haɗu da Allah (S.W.A.) ranar alƙiyama.

9. Azumi garkuwa ne daga wutar Jahannama. Yana kare mutum daga sharrin sha’awa da zunubi.

10. A Ramadan, Allah Yana ’yantar da bayinsa daga wuta. Duk wani dare, Allah Yana yafe wa bayinsa kuma yana kuɓutar da su daga azabar lahira.

Wannan wata mai albarka yana ƙarfafa imani, ibada, da kyautatawa.

Don haka, ya kamata Musulmi su yi amfani da watan Ramadan don samun kusanci ga Allah da aikata kyawawan ayyuka.