Falalar Watan Al-Muharrama: A dage da yin addu’oi na musamman —Gwamnonin Arewa
Gwamnonin Arewa sun hori al’ummar Musulmi su yi amfani da falalar watan Al-Muharrama na sabuwar shekarar Musulunci ta 1446 Bayan Hijira wajen yin adduo’oi na musamman don samun sauki a Najeriya
Shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa, Gwamnan Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, ya hori al’ummar Musulmi su yi amfani da falalar watan Al-Muharrama na sabuwar shekarar Musulunci ta 1446 Bayan Hijira wajen yin adduo’oi na musamman don samun ruwan sama.
Inuwa Yahaya ta hannun kakakinsa. Isma’ila Uba Misilli, a ranar Lahadi, ya jaddada muhimmancin hadin kai da zaman lafiya, yana mai cewa ana bukatar ruwa a lokacin da damuna ta yi nisa, amma har yanzu ruwan bai samu sosai ba a wasu yankunan.
Ya bayyana cewa sabuwar shekarar musulunci shekara ce da za ta tuna wa Musulmi baya da fatan cewa za su sadaukar da komai ga Allah da kyakkywan niyya domin Allah Ya tausaya wa bayinSa.
A cewar sanarwar, ana cikin matsancin kuncin rayuwa a Najeriya, wanda hakan ke nuna mahimmancin hadin kai da taimakon juna a tsakanin al’umma.
- Sai Atiku, Obi da Kwankwaso sun yi maja za su kayar da Tinubu — Lukman
- NAJERIYA A YAU: Dalilin Dawowar Layukan Mai A Najeriya
Sannan ya tabbatar wa da al’umma cewa gwamnati tana iya kokarin ta wajen ganin ta samar musu da ayyukan raya kasa da kuma ciyar da tattalin arziki gaba.
Daga nan sai ya ce yana da yakinin cewa wannan sabuwar shekara za ta shigo da kyawawan alhkairi wa kasa don haka mutane su karfafa imanin su wajen gudanar da addu’oi alheri da sa tsoron Allah a dukkan lamuransu.