Falalar yawaita Istigfari

Babu wata damuwa ko matsala da yawan Istigfari ba ya kawar da ita.

Falalar yawaita Istigfari

Ayoyin Kur’ani da Hadisan manzon Allah SAW da yawa sun bayyana falalar yawaita neman gafara daga wurin Allah Madaukakin Sarki.

Neman yafiyar Allah da tuba bisa laifukan da bawa ke yi yana da tasiri a rayuwar bawa ta yau da gobe kamar yadda Alkur’ani mai tsarki ya kawo a wurare da dama.

Manzannin Allah gaba daya sun kira al’ummominsu da su kasance sun­  yawaita ambaton Allah tare da neman afuwa da kuma neman yardarSa.

Cikin Alkur’ani Allah SWT ya ce, mu nemi gafararSa Shi kuma zai gafarta mana. Bugu da kari Zai yalwata mana arziki da samar mana da jin dadin duniya da na lahira.

An ruwaito ciki hadisi cewar Manzon Allah yakan yi istigfari a rana sama da sau 70, a matsayinsa na Annabi da Allah ya tabbatar masa da yafiya da kuma yardarsa.

Falalar yawaita istighfari sun hadar da:

Kankare zunubai

Yalwar arziki da dukiya

Samun haihuwa da yawan ’ya’ya

Samun nutsuwar zuciya

Samun damina mai albarka

Saukaka alamarin bawa a rayuwarsa

Bawa zai samu rabaita da gidan Aljanna

Wani babban malami ya ce babu wata damuwa ko matsala da ya taba shiga face ya tunkare ta da yawan neman gafarar Allah kuma cikin ikonSa Yana kawo masa sauki.