Falalar zikiri (1)
Da sunan Allah Mai rahama Mai jin kai. Tsira da Amincin Allah su kara tabbata ga fiyayyen halitta, shugabanmu Annabi Muhammad da alayensa da sahabbansa baki daya. Bayan haka, yau cikin yardar Allah za mu gabatar da wani abu ne a kan falalar zikiri wato ambaton Allah da tunawa da Allah a cikin dukan al’amuranmu. […]
Da sunan Allah Mai rahama Mai jin kai. Tsira da Amincin Allah su kara tabbata ga fiyayyen halitta, shugabanmu Annabi Muhammad da alayensa da sahabbansa baki daya.
Bayan haka, yau cikin yardar Allah za mu gabatar da wani abu ne a kan falalar zikiri wato ambaton Allah da tunawa da Allah a cikin dukan al’amuranmu.
Hakika zikiri ko ambaton Allah yana daga cikin mafiya tsarkakan ayyuka da kyawawansu da girmansu kuma mafiya soyuwa a wurin Allah Azza Wa Jalla. Tirmizi da sauransu sun ruwaito daga Abu Darda’u (RA) ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce: “Ashe ba zan ba ku labarin mafi alherin ayyukanku kuma mafi tsarkinsu (dadinsu) a wurin Mamallakinku kuma mafi daukakawa ga darajojinku kuma mafi alheri gare ku daga ciyarwarku ga zinari da takardun kudadenku ba, kuma mafi alheri gare ku a ce kun hadu da abokan adawarku su doki wuyayenku ku doki wuyayensu ba?” Sai suka ce: “Hakika muna so ka ba mu (wannan labari) ya Manzon Allah!” Sai ya ce: “Zikirin (ambaton) Allah Madaukaki.”
Masu ambaton Allah, masu tunawa da Allah su ne a kan gaba wurin tafiya don haduwa da Allah da kuma Ranar Lahira lami lafiya. An karbo daga Abu Huraira (RA) daga Annabi (SAW) ya ce: “Masu kadaitawa sun wuce gaba. Suka ce su wane ne masu kadaitawa ya Manzon Allah?” Ya ce: “Masu ambaton Allah da yawa maza da masu ambato (da yawa) mata.” Wadannan su ne -bayin Allah- wadanda Allah Ya yi musu tattalin masauki mai girma da lada mai girma. “Masu zikiri (ambato da tuna) Allah da yawa maza da masu zikiri mata, Allah Ya yi musu tattalin wata gafara da wani lada mai girma.” (Ahzab: 35).
Ambaton Allah wato zikiri shi ne yake raya zukata, zukata ba su rayuwa sai da shi, Buhari ya ruwaito a cikin sahihinsa daga Abu Musa Al’ash’ari (RA) daga Annabi (SAW) ya ce: “Misalin wanda yake ambato ko tuna Ubangijinsa da wanda ba ya ambato ko tuna Ubanginsa kamar misalin mai rai ne da matacce.”
Hakika zukata ba za su samu tabbatuwa da natsuwa ba, ko su samu jin dadi su samu sa’ada ba, sai tare da zikirin Allah da tunawa da Shi. Allah Madaukaki Yana cewa: “Wadanda suka yi imani, zukatansu suna (samun) natsuwa ne da ambaton Allah. Ku saurara! Da ambaton Allah (zikiri) zukata suke samun natsuwa.” (Ra’ad: 28).
Ambaton Allah shi ne ke kawo mafita a bayan kunci, ya kawo sauki a bayan tsanani, ya kawo farin ciki a bayan wahala da damuwa. Shi yake kwaranye abubuwan da suke kawo bakin ciki ya saukaka al’amura ya tabbatar da raha da sa’ada a duniya da Lahira. Babu abin da yake magance bakin ciki ya gusar da tsanani kamar ambaton Allah da zikirin Allah Madaukaki. Annabinmu (SAW) ya kasance a duk lokacin da wani abin bakin ciki ya same shi yana cewa: “La ilaha illallahul azim, la ilaha illallahul halim. La ilaha illallahu rabbus samawati wa rabbul arshil karim.” Ma’ana: “Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Mai girma. Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Mai hakuri. Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Ubangijin sammai kuma Ubangijin kasa kuma Ubangijin Al’arshi Mai girma.” Sannan Mai Tsira da Amincin Allah yana cewa: “Addu’ar ma’abucin kifi: “La ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minaz zalimina.” Ma’ana: “Babu abin bautawa da gaskiya sai Kai, Tsarkinka ya tabbata, lallai ni na kasance daga cikin azzalumai.” Babu wanda zai fada a cikin bakin ciki da zai yi addu’a da ita face an kwaranye masa bakin cikinsa.”
Zikiri yana jawo ni’imar da ta kubuce wa bawa kuma ya kiyaye tare da tsare ni’imar da mutum yake da ita. Kuma babu abin da yake jawo ni’ima ya tsare ta irin zikirin Allah Madaukaki. “Kuma a lokacin da Ubangijinku Ya sanar, “Lallai ne idan kun gode, hakika Ina kara muku, kuma lallai ne idan kuka kafirta hakika azabaTa, tabbas mai tsanani ce.” (Ibrahim: 7).
Daga cikin falalar zikiri akwai shafe laifuffuka da kankare miyagun ayyuka da daukaka darajoji da kuma samun daukaka a wurin Allah Madaukaki. Tirmizi ya ruwaito daga Annabi (SAW), ya ce, “Babu wani aiki da dan Adam zai yi da ya fi saurin kubutar da shi daga azabar Allah kamar zikirin Allah.” Kuma ya tabbata daga gare shi (SAW) cewa lallai shi ya ce: “Wanda ya ce, “Subhanallahi wa bi hamdihi” sau dari an shafe laifuffukansa koda sun kai misalin kumfar teku ne.” Irin wadannan hadisai kan wannan batu suna da yawa.
Sannan daga cikin falalar zikiri akwai cewa, shi shuka ce a cikin Aljanna. Mutum ba ya shuka a cikin Aljanna da abin da ya kai zikiri ko ambaton Allah. Annabi (SAW) yana cewa: “Wanda ya ce: “Subhanallahi wa bi hamdihi” za a shuka masa wata dabiniya a cikin Aljanna.” Tirmizi ya ruwaito. Kuma Tirmizi (RA) ya sake ruwaitowa daga Annabi (SAW), ya ce: “Na hadu da Annabi Ibrahim Khalil a daren da aka yi Isra’i da ni. Sai ya ce min: “Ya Muhammad! Ka isar min da gaisuwata zuwa ga al’ummarka, (ya siffanta masa Aljanna, sannan a karshen Hadisin, ya ce,) “Ka ba su labari cewa: “Lallai shukarta ita ce: “Subhanallahi, walhamdulillahi wa la ilaha illallahu wallahu akbar.”
Zikiri dai kalmomi ne masu saukin fadi a baki, ba su wahalar da bawa ko su zame masa nauyi, amma kuma suna da lada mai girma da ijara mai yawa. Sannan su kalmomin nan ababen so ne a wurin Allah Madaukaki. Buhari (RA) ya ruwaito a Sahihinsa daga Annabi (SAW) cewa lallai shi ya ce: “Kalmomi biyu masu sauki a kan harshe, amma masu nauyi a kan mizani, sannan masu girma a wurin Mai rahama. Su ne: “Subhanallahi wa bihamdihi, subhanallahil azim.”
Sannan zikiri da ambaton Allah na kore shaidanu daga kusa da bawa, na tsare bawa daga wasi-wasin shaidanu da sharrukansu da kaidojinsu da duk miyagun tuggunsu. Allah Madaukaki Ya ce: “Kuma idan wata fizga ta fizge ka daga Shaidan, to ka nemi tsari daga Allah. Lallai Shi, Shi ne Mai ji, Masani.” (Fussilati: 36). Kuma Allah Ya ce: “Ka ce: “Rabbi inni a’uzu bika min hamazatis shayadini. Wa a’azu bika Rabbi an yahdurun.” (Ma’ana: Ya Ubangijina, ina neman tsari da Kai daga fizge-fizgen shaidanu. Kuma ina neman tsari da Kai, ya Ubangijina! Domin kada su halarto ni.)” (Mu’umiun: 97-98). Kuma Ya sake cewa: “Lallai ne wadanda suka yi takawa, idan wani tashin hankali daga Shaidan ya shafe su, sai su tuna (Allah), sai ga su sun zama masu basira.” (A’araf: 201). Kuma Ya sake cewa: “Kuma wanda ya makanta daga barin tuna (ambaton) Mai rahama, to za Mu lullube shi da Shaidan wato shi ne abokinsa.” (Zukhuruf: 36).