Falalar zikiri (2)
Kuma nassoshi da dama sun nuna cewa mafi falalar zikiri shi ne fadin La’ilaha illallah, don haka akwai ya kamata kullum harshen Musulmi ya kasance jike da fadin La’ilah illallah. Duk lokacin da mutum ya gafala daga ambaton Allah, sai Allah Ya mance da shi, daga nan kuma sai Shaidan ya samu galaba a kansa. […]
Kuma nassoshi da dama sun nuna cewa mafi falalar zikiri shi ne fadin La’ilaha illallah, don haka akwai ya kamata kullum harshen Musulmi ya kasance jike da fadin La’ilah illallah. Duk lokacin da mutum ya gafala daga ambaton Allah, sai Allah Ya mance da shi, daga nan kuma sai Shaidan ya samu galaba a kansa. Kalmar La’ilaha illallah, kalma ce mai saukin fadi a kan harshe, mai nauyi a wurin Allah.
Ya zo a cikin Hadisi cewa: “Lallai Annabi Musa (AS) ya ce: “Ya Ubangiji! Ka koya min wani abu da zan ambace Ka da shi kuma in roke Ka da shi. Sai (Allah) Ya ce: “Ya Musa ka ce: “La’ilaha illallah!” Sai Musa ya ce: “Ya Ubangiji! Dukan bayinKa suna fadin wannan.” Allah Ya ce: “Ya Musa! Da sammai bakwai da abin da ke raye a cikinsu koma bayaNa da kassai bakwai da abin da ke raye a cikinsu koma bayaNa, za su kasance a kunnen daya na sikili, kuma La’ilaha illallah, ta kasance a daya kunnen sikelin, to, La’ilaha illallahu za ta rinjaye su!”
Kalmar La’ilaha illallah, kalma ce mai girma, kuma tana da ma’auninta a wurin Allah, ba kalma ce ta lafazi kawai ba, kalma ce mai ma’ana da manufa da wajibi ne Musulmi ya san ma’anar kuma ya yi aiki da manufarta. Ma’anar ita ce: “Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah – duk wani abin bauta koma bayanSa batacce ne. Da kalmar La’ilaha illallah, aka aiko dukan Manzanni (AS), kamar yadda Allah Ya tabbatar da haka a cikin fadinSa: “Kuma ba Mu aiki wani Manzo ba a gabaninka face Muna yin wahayi zuwa gare shi cewa: “Lallai ne shi, babu abin bautawa da gaskiya face Ni, sai ku bauta Mini.” (Anbiya: 25).
Don haka ba furta kalmar kawai ba, akwai wajibcin Musulmi ya san ma’anar kalmar La’ilaha illallahu, kuma ya yi aiki da ita domin tana kore dukan nau’o’in shirka da dukan ababen bauta ta tabbatar da bautar ga Allah Shi kadai. Wajibi ne mutum ya fade ta da harshe kuma ya tabbata ya tsarkake ta a cikin zuciyarsa. Hadisi ya zo daga Abu Huraira (RA) lokacin da ya tambayi Manzon Allah (SAW) cewa: “Ya Manzon Allah! Wane ne mafi rabauta da cetonka a Ranar kiyama? Sai (SAW) ya ce: “Wanda ya ce, La’ilaha illallahu yana mai tsarkake ta a cikin zuciyarsa.” Ma’ana ba kawai ya fade ta da harshe ba ne a’a har cikin zuciyarsa haka yake nufi. Kuma a wani Hadisin ya ce: “Lallai ne Allah Ya haramta wa wuta wanda ya ce La’ilaha illallah, yana mai nufin yardar Allah da haka.” Ba wai ya fadi haka da harshe kawai ba ne, a’a ya kiyaye duk abubuwan da take nufi. Domin lokacin da Annabi (SAW) ya ce da mushirikai ku ce “La’ilah illallahu, za ku rabauta.” Saboda sun san ma’ana da manufarta sai suka ce: “Shin ya sanya gumaka (ababen bauta) su zama abin bautawa guda? Lallai wannan hakika wani abu ne ake nufi!” (Sad:5). Kuma Allah Ya sake cewa: “Lallai su sun kasance idan an ce musu, “La’ilaha illallahu – Babu abin bautawa da gaskiya face Allah,” sai su dora girman kai.” (Saffat: 35).
Mutanen Jahiliyya sun ki amincewa su fadi wannan kalma ce, saboda sun san za ta raba su da gumakansu ta bata bautarsu ga gumaka su kuma ba su son barin bauta wa gumakansu, sun fi son su ci gaba da rike su.
Har wa yau zikiri yana raya gidaje, Annabi (SAW) ya ce: “Misalin gidan da ake ambaton Allah a cikinsa da gidan da ba a ambaton Allah a cikinsa, kamar misalin rayayye ne da matacce.”
Ayoyi da dama da kuma Sunnar Annabi (SAW) suna karfafa mana tare da ingiza mu zuwa ga yin zikiri da ambato da tuna Allah. Kuma suna umartar mu a kan yin zikirin da yawa tare da yi mana bayanin irin ladaddakin da masu yawaita zikiri suke samu a cikin ayoyi masu yawa da hadisai da dama.
Allah Madaukaki Yana cewa: “Ya ku wadanda suka yi imani! Ku ambaci Allah, ambato mai yawa. Kuma ku tsarkake Shi a safiya da maraice. (Allah) Shi ne Wanda Yake yi muku salati (tsarkake ku) da mala’ikunSa (su ma suna yi muku addu’a), domin Ya fitar da ku daga duffai (na kafirci da gafala) zuwa ga haske (na imani da tsarkaka). Kuma Allah Ya kasance Mai jin kai ga muminai.” (Ahzabi: 41- 43).
Ibn Abbas (RA) ya ce: “Idan kuka aikata haka – ma’ana kuka yawaita zikiri ko ambaton Allah Madaukaki – Sai Allah Ya yi muku salati (addu’a, Shi) da mala’ikunSa.”
Kuma Allah Madaukaki Ya sake cewa: “Masu ambaton Allah (zikiri) da yawa maza da masu ambaton Allah da yawa mata, Allah Ya yi musu tattalin wata gafara da wani sakamako mai girma.” (Ahzab: 35). Kuma Ya sake cewa: “Kuma ku ambaci Allah da yawa, tabbas za ku samu nasara.”( Anfal: 45). Da sauran ayoyi da hadisai masu yawa da suke kwadaitarwa da karfafa Musulmi su yawaita ambaton Allah kuma suke umartarsu da ambatonSa da yawa.
Malamai sun fadi a cikin littattafan tafsiri da sharhohin hadisai cewa: “Idan Musulmi ya lizimci azkar (zikirorin) asuba da maraice da na bayan sallolin farilla da na kwanciya da azkar din da ake yi lokacin shiga ko fita daga gida ko kasuwa da wadanda ake yi lokacin bakin ciki da lokacin cin abinci da abin sha da bayan kammala ci ko shan su da sauran zikirorin da ake bukatar Musulmi ya rika yi a dare da ranarsa tare da lurarsa da zikiri mudalaki, za a rubuta shi a ckin masu ambaton (zikirin) Allah da yawa maza da masu ambaton Allah da yawa mata, wadanda Allah Ya yi musu tattalin wata gafara da wani lada mai girma.
Kuma wata falalar zikirin ita ce, cewa Allah Yana tunawa da duk mai ambatonSa kamar yadda Ya ce: “Saboda haka ku tuna Ni, In tuna ku.” (Bakara:152). Ko da a ce wannan ne kawai alfanun da ke cikin zikiri ya isa falala da daukaka ga ma’abucinsa. A wani Hadisin kudusi, Annabi (SAW) ya ce Allah Ya ce: “Ina inda bawaNa yake tsammaniNa, kuma Ina tare da shi idan ya tuna da Ni. Idan ya ambace Ni ko ya tuna da Ni a cikin zuciyarsa, sai In tuna da shi a zuciyaTa. Idan ya tuna da Ni a cikin taron jama’a, sai In tuna da shi a cikin taron da ya fi wancan alheri.” Buhari da Muslim suka ruwaito.
Alheran zikiri ga masu yin sa da fa’idojinsa a kan masu tsare shi suna da yawa, idan mutum yana so ganin haka yana iya duba littattafan da malamai suka rubuta a kan wannan babi mai girma, musamman littafin Al-Wabilus Sayyib Min Kalamid dayyib na Allama Ibn kayyim Aljauziyya (Allah Ya yi masa rahama). A ciki ya ambaci manyan fa’idojin zikiri kuma ya ce: “A cikin zikiri akwai kimanin fa’idoji kusan dari.” inda ya jero su daki-daki.
Ko wadannan fa’idoji kawai ka tsaya a kansu za ka kara kwadayi game da yawaita zikiri da tsare yin sa a kowane lokaci.
Wannan kadan ne daga cikin falalar zikiri ga Musulmi, bai kamata Musulmi ya shagaltu da wasu harkoki na duniya a ce sun dauke masa hankali daga zikiri da ambaton Allah ba, musamman yanzu da muka shiga hargiwar facebook da Instgram da tweeter da makamantansu ba. Maimakon mu yi amfani da su ta hanyar da ta kamata wajen nemo abubuwan da za su kusanta mu da Allah mu kasance cikin ambatonSa a kowane lokaci sai muka koma tabo harkokin duniya da baragada da soke-soken juna kan abubuwan duniya da sauransu. Mai hankali dai shi ne wanda ya tilasta ransa ga aikata abin da zai amfane shi a bayan mutuwarsa, tababbe marar wayo shi ne wanda ya bi son ransa ya rika bin rudin duniya da dogon buri har ya mance Allah, kuma Allah Ya mance da shi.