Falaloli 12 da ya kamata ku sani kan Ranar Arafa

A wunin Allah Ya cika addinin Musulunci, kuma shi ne wuni mafi alheri a cikin shekara

Falaloli 12 da ya kamata ku sani kan Ranar Arafa

Masu Aikin Hajji a kan Dutsen Arfa

Wunin Arafa daya ne daga cikin wuni goma na farkon watan Zulhijja wanda Hadisi ya tabbatar cewa babu wasu wuni mafiya falala sama da su a cikin shekara.

A yayin da alhazai ke fita zuwa filin Arafa domin tsayuwa a tsawon wunin suna gudanar da ayyukan ibada, wadanda ba su samu hali ba kuma an karfafe su da yin azumi domin ribata daga falalar wannan yini mai dimbin falala.

Wadannan sun hadar da:

  1. Shi ne wuni mafi  falala a cikin shekara.
  2. A wunin Allah Ya cika addinin Musulunci.
  3. Allah Ya yi rantsuwa da wunin a cikin Suratul Buruj.
  4. A cikin wunin Allah na ’yanta bayi daga wuta zuwa aljanna.
  5. A wunin alhazai ke taru a wuri daya domin tsayuwa a filin Arafa
  6. A ranar Allah kan yi alfahari da bayinsa da suka halarci tsayuwar Arafa.
  7. Babu aikin Hajji ga mahajjacin da bai yi tsayuwar Arafa a cikin wunin ba.
  8. Azumtar wunin na kankare zununban shekara da ta gabata da mai wanzuwa.
  9. Wuni ne mai albarka da zama silar mutum ya samu aljannah.
  10. A irin wannan yini Manzon Allah (SAW) ya yi hudubarsa ta bankwana
  11. A cikin wunin ake samun mafi alherin addu’a. Manzon Allah ce shi da dukkanin manzannin da suka gabata sun yi addu’ar da ta fi kowacce falala: “La ilaha illal Lahu wahdaHu la sharika laHu laHul mulku wa laHul hamdu wa Huwa ala kulli shai’in kadir.”
  12. Yana da kyau a kara da dukkan ayyukan alheri, gaida mara lafiya, karatun Al Kur’ani