Falasɗinawa fiye da 300,000 sun rasa matsuganansu a Zirin Gaza — MDD

MDD ta yi gargaɗin cewa abinci da ruwa na daf da ƙarewa a Gaza.

Falasɗinawa fiye da 300,000 sun rasa matsuganansu a Zirin Gaza — MDD

Majalisar Dinkin Duniya ta ce sama da mutane dubu dari 3 da 38 ne luguden wutar da Isra’ila ke ci gaba da yi a kan Gaza ya tilasta musu barin gidajensu.

A gefe guda kuma, mahukuntan yankin suka ce adadin wadanda suka mutu a bangarensu ya kai dubu 1 da dari 2.

A wata sanarwar Hukumar Kula da Ayyukan Jinkai ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce zuwa daren Laraba, adadin wadanda luguden wutar Isra’ila ya ɗaiɗaita a yankin Gaza ya karu da kimanin mutane dubu 75, daga wanda ta bayar tun da farko, inda a yanzu adadin ya kai dubu dari 3 da 38 da dari 9 da 34.

Wannan na zuwa ne a dai dai lokacin da Isra’ilar ke ci gaba da luguden wuta a kan wuraren da take ganin sansanonin mayakan kungiyar Hamas ne a yankin na Gaza, yankin da ke da yawan al’umma miliyan 2 da dubu dari 3, a matsayin martani ga hari mai ban mamaki da Hamas ta shammace ta da shi a ranar Asabar.

A bangare guda alkaluman wadanda suka mutu a yakin na Hamas da Isra’ila, bangaren yahudawa akwai mutane dubu 1 da 200 galibi fararen hula baya ga sojoji kusan 200 sai kuma a harin mafi muni da Isra’ilan yahudu ta taba fuskanta a tarihi.

A bangaren Gaza kuwa ma’aikatar lafiyar yankin ta ce adadin wadanda suka mutun ya kusa dubu 1 da 200 lura da yadda Sojin Isra’ila ke ci gaba da luguden wuta a lungu da sako na birnin.

‘Mun ba wa Falasɗinawa wa’adin kwana daya su fice daga Zirin Gaza’

Kawo yanzu dai sra’ila ta shaida wa Majalisar Dinkin Duniya cewa dole duk Falaɗinawan da ke Arewacin Zirin Gaza su tsallaka zuwa Kudanci cikin sa’o’i 24.

Tankokin yaƙin Isra’ila sun ƙara kusantar iyakar Gaza, gabanin afkawa birnin don kawar da mayakan Hamas.

Ofishin Majalisar Dinkin Duniya a Gaza ya ce dakarun Isra’ila ne suka gabatar da wannan gargaɗi a cikin daren Alhamis.

Wannan na zuwa ne yayin da dakarun Isra’ila suka ci gaba da ludugen wuta a Gaza, yayin da aka shiga rana ta biyu da katse wutar lantarki a yankin da Falasɗinawa suke.

Haka nan kuma, Majalisar Dinkin Duniya ta ce ta damu matuƙa da yadda mata masu juna biyu da yawan su ya kai dubu goma sha biyar a Gaza ba su samun zuwa asibiti don kula da lafiyarsu, ga kuma rashin ruwa mai tsafta.

Ma’aikatan lafiya sun ce mutane aƙalla 45 aka kashe, yayin da ɗaya daga cikin hare-haren ya rusa rukunin gidaje a Jabaliya.

Wasu daga cikin mutanen da lamarin ya ritsa da su sun shiga gidajen ne don neman mafaka daga luguden bama-baman.

Alkalumma sun bayyana cewa mutane fiye da dubu daya da dari biyar hare-haren sama na Isra’ila suka kashe tun daga ranar Asabar da ta ƙaddamar da su.

Isra’ila ta ce ba za ta yi sassauci ba kan rufe duk wata hanyar shigar da kayan agaji zuwa Gaza har sai mayaƙan Hamas sun saki waɗanda suka yi garkuwa da su, duk da cewa shirin samar da abinci na Majalisar Dinkin Duniya ya yi gargaɗin samun ƙarancin abinci da ruwa a Gazar.

Ana sa ran fiye da rabin su za su haihu a cikin watanni masu zuwa.

Jami’an Majalisar Dinkin Duniyar sun kuma bayyana damuwa da halin da matan za su shiga saboda tsananin fargaba da damuwa.