Falasɗinawa miliyan ɗaya na rige-rigen ficewa daga Zirin Gaza

Netanyahu ya sha alwashin cewa sai sun ruguza duk wani yanki da Hamas ke ciki.

Falasɗinawa miliyan ɗaya na rige-rigen ficewa daga Zirin Gaza

Falasɗinawa da ke zaune a arewacin yankin Zirin Gaza, na rige-rigen ficewa daga yankin yayin da wa’adin sa’a 24 da Isra’ila ta ba su su fice ke karatowa.

Isra’ila ta ba fararen hula da ke arewacin yankin umarnin su fice yayin da ake fargabar tana shirin kutsawa cikin Gaza don fafatawa da mayakan Hamas.

Akalla fararen hula sama da miliyan daya ake tunanin za su fice domin komawa kudancin yankin.

Hamas ta yi watsi da gargadin na Isra’ila wanda ta kira farfaganda.

A ranar Juma’a dakarun tsaron Isra’ila na IDF suka ba da tabbacin cewa sun sanar da mazauna birnin Gaza kan su fice “domin kare lafiyarsu.”

“Za ku iya dawowa yankin na Gaza idan muka fitar da sanarwa hakan,” Kakakin IDF Laftanar Kanar Jonathan Conricus ya ce.

Kamfanin Dillancin Labarai na AP ya ruwaito kungiyar ta Hamas tana kira ga al’ummar yankin “da su zauna a gidajensu su kuma tsaya-tsayin daka saboda sanarwar ta farfaganda ce.”

Jakadan Falasdinu a Majalisar Dinkin Duniya, Riyad Mansour, ya fadawa manema labarai a ranar Juma’a cewa, umarnin da Isra’ila ta bayar na ficewa, daidai yake da “kisan kare dangi” na daruruwan dubban Falasdinawa wadanda babu inda za su iya zuwa.

Isra’ila ta jibge dakarunta dubu 300 a kusa da iyakarta da Gaza, amma kuma ta ce ba ta yanke shawarar kan ko za ta kutsa cikin yankin ba.

Sai dai ta ci gaba da yin luguden wuta a Gaza, inda ta ce ba za ta kakkauta ba har sai Hamas ta saki Yahudwa 150 da ta kama.

A ranar Asabar din da ta gabata, mayakan Hamas suka kai wani harin ba-zata a kudancin Isra’ila lamarin da ya sanadin mutuwar daruruwan Yahudawa.

A hare-hare martanin da ta kai, Isra’ila ita ma ta halaka daruruwan Falasdinawa tare da katse hanyoyin wutar lantarki, ruwa da man fetur.

Dakarun Isra’ila sun shiga Gaza

Sojojin kasar Isra’ila a karon farko sun sanar da cewa dakarunsu sun kutsa kai cikin Zirin Gaza domin kai harin kan kungiyar Hamas.

A cikin wata sanarwa a ranar Juma’a, sojojin sun ce sun shiga Gazan ne domin su yaki ’yan Hamas, su lalata makamai sannan su kuɓutar da Yahudawan da Hamas ta yi garkuwa da su.

Sanarwar ta ce sun fara kai samame wasu unguwannin Zirin Gaza yayin da dakarunsu ke shirin kai gagarumin farmaki ta ƙasa.

Sai dai sanarwar na nuna cewar akwai alamun ci gaba da dauki-ba-dadi a nan gaba kadan.

Sai mun ruguza duk wani yanki na Hamas — Netanyahu 

Da yake jawabi kafin ƙaddamar da luguden martani a kan Hamas, Firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, ya ce harin na jiragen sama somin-taɓi ne kuma a yanzu Isra’ila na yaƙi ne don kare kanta.

A wani jawabi da ya yi wa jama’ar ƙasar, Mista Netanyahu ya ce kawo yanzu rundunarsa ta kai hari kan matsugunnan Hamas fiye da dubu biyu a Gaza.

Ya sha alwashin cewa sai sun ruguza duk wani yanki da Hamas ke ciki.

Ya ce “Mummunan harin da Hamas ta kai kan Isra’ilawan da ba su ji ba basu gani ba, ba ƙaramin abin tashin hankali bane.

“Sun kashe iyalai a gidajen mu, sun hallaka ɗaruruwan matasa da suka taru domin wani biki, sun kuma yi garkuwa da mata da yara da kuma tsofaffi. Sun kai hari kan ƙananan yara kuma sun ƙona wasu da dama,” in ji shi.