Falasdinawan da Isra’ila ta kashe a Gaza sun haura 30,000

Ma’aikatar lafiya ta Zirin Gaza ta ce sojojin Isra’ila sun kashe fararen hula 104, sun jikkata wasu fiye da 750 a wurin karbar kayan agaji

Falasdinawan da Isra’ila ta kashe a Gaza sun haura 30,000

Wani Bafalasdine a lokacin da ake kula da shi a asibitin Kamal Edwan, bayan sojojin Isra’ila sun bude wa fararen hula wutaa wurin karbar kayan agaji a yankin Beit Lahia da ke Arewacin Zirin Gaza a ranar 29 ga Fabarairu, 2024 (Hoto: AFP)

Ma’aikatar lafiya ta Zirin Gaza ta ta sanar cewa mutane 104 ne suka mutu, wasu fiye da 750 suka jikkata bayan sojojin Isra’ila sun bude wuta kan fararen hula da suka taru a wurin karbar kayan agajin yankin Falasdinu.

Kakakin ma’aikatar, Ashraf al-Qudra, ya ce adadin wadanda suka mutu sakamakon “kisan gillan” na ranar Alhamis a birnin Gaza ya haura zuwa shahidai 104 da kuma jikkata 760 sakamakon harbin da sojojin Isra’ila suka yi wa taron jama’an a yankin Nabulsi.

Majiyoyin Isra’ila sun tabbatar da harbin, tare da cewa sojojin sun bude wuta ne bayan da suka yi zargin barazana daga taron jama’a da ke kusa da wurin karbar kayan agajin.

Ma’aikatar ta ce zuwa adadin mutanen Isra’ila ta kashe a Gaza ya zarce 30,000 daga lokacin da Isra’ila ta fara kai hari a yankin a watan Oktoban 2023 zuwa yanzu.

Kwararru dai na ganin adadin ba shi ne hakikanin alkaluman wadandana aka kashe ba, lura da yadda ake wahalar samun bayanan mace-mace a yanayin yaki da kuma katsewar sadarwa da rugujewar tsarin kiwon lafiya a Gaza.

NLC ta yi watsi da ƙara kuɗin kiran waya da data

DSS ta gurfanar da Mahdi Shehu kan zargin ta’addanci

Sojoji sun kashe mataimakin Bello Turji

Harin ’Yan Fashi: Buni ya jajanta wa ’yan kasuwar Ngalda