Falken wiwi mai amfani da kakin ’yan sanda ya shiga hannu
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ta yi nasarar cafke wani dan sandan bogi mai mukamin ASP da sunan Ayodele Adegoke mai fakewa da kakin ’yan sanda yana fataucin tabar wiwi.Wanda ake zargin ya ce shi ba dan sanda ba ne, kuma kakin da yake sakawa na wani yayansa ne da ya rasu.Ayodele ya bayyana haka […]
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ta yi nasarar cafke wani dan sandan bogi mai mukamin ASP da sunan Ayodele Adegoke mai fakewa da kakin ’yan sanda yana fataucin tabar wiwi.
Wanda ake zargin ya ce shi ba dan sanda ba ne, kuma kakin da yake sakawa na wani yayansa ne da ya rasu.
Ayodele ya bayyana haka ne a hedikwatar ’yan sandan Jihar Kaduna lokacin da aka gabatar da shi ga manema labarai a karshen makon jiya.
Ya ce Shaidan ne ya tura shi ga wannan aiki ya kuma ce haramta sana’ar acaba da Gwamnan Jihar Legas Babatunde Fashola ya yi ne ya sa ya shiga wannan harka bayan ya koma Jihar Ondo.
“Ina sana’ar acaba ne a Jihar Legas kafin a haramta ta daga nan sai na koma garinmu a Jihar Ondo. Da na shiga dakin yayana da ya rasu mai suna Goke sai na dauki rigarsa ta ’yan sanda sai wani ya ba ni shawarar sano’o’in da zan iya yi da rigar. Ya ce ina iya yin safarar motoci da kuma tabar wiwi. Tafiyar da na fara yi na farko ita ce daga Abuja zuwa Ondo kuma a duk shingayen da na tarar a hanya suna girmama ni sannan su bar ni in wuce. Na kai tabar wiwi ta farko ne Abuja wajen wani Alhaji Yusuf da ke Gwagwalada shi kuma ya biya ni Naira dubu 90.”
Ya ce a tafiyata ta biyu ya kai tabar da wani Alhaji a Zariya a kan Naira dubu 130, kuma a yayin da yake kusa da shiga Zariya ne, ya lura motar da yake ja wadda ta surukinsa ne ta samu matsala. Kuma lokacin da ya tsaya domin duba motar sai wata motar ’yan sanda ta zo ta tsaya kusa da shi domin su taimaka masa saboda kakin da yake sanye da shi. “Ni kuma a zuciyata sai addu’a nake yi su tafi da matsalarsu daga baya har sun tafi sai kuma suka sake dawowa suna yi min wasu tambayoyi ni kuma na kasa ba su gamsasshiyar amsa daga nan ne suka kama ni,” inji shi.
A cewar ’yan sandan sun kuma yi nasarar kama wata tankar dakon man fetur mai lamba LSD 768 dM a Maraban Jos cike da tabar wiwi sun kuma ce a lokacin da direbobin motar suka hango ’yan sandan sun gudu suka bar tankar da suka binciki motar ce suka gano buhunhunan wiwi 70. Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Kaduna Umar Shehu ya ce rundunar na ci gaba da bincike domin gano direbobin.
Kwamishinan ya gabatar da wasu ’yan fashi da rundunar hadin gwiwa na yaki da ’yan fashi da makami ta kama a sassan jihar.