Fallasa magudin zaben Ekiti: Yadda sojoji suka ci zarafin dan uwana – Kyaftin Koli
Kyaftin Sagir Koli, wani jami’in soja da ya fallasa yadda aka shirya magudin zaben Gwamnan Jihar Ekiti na bara, inda wasu manyan jami’an gwamnati da na soji suka yi zaman tattauna yadda za a mured zaben Jam’iyyar PDP ta samu nasara, ya ce sojoji sun kama kanensa suka ba shi wahala a wani barikinsu da […]
Kyaftin Sagir Koli, wani jami’in soja da ya fallasa yadda aka shirya magudin zaben Gwamnan Jihar Ekiti na bara, inda wasu manyan jami’an gwamnati da na soji suka yi zaman tattauna yadda za a mured zaben Jam’iyyar PDP ta samu nasara, ya ce sojoji sun kama kanensa suka ba shi wahala a wani barikinsu da ke Ibadan fadar Jihar Oyo, bayan shi ya gudu da kasar nan.
Wani faifan bidiyo da jaridar Premium Times ta ce ta samu a ranar Litinin, ya ruwaito Kyaftin Koli yana cewa, kanensa Adamu Koli mai shekara 15 wanda suke zaune tare kafin ya gudu, an kama shi ne a gidansa da ke Akure ta Jihar Ondo inda yake aiki.
“Yana zaune da ni kuma yana makarantar yaran sojoji da ke barikin, sun je sun kama shi bayan sun samu labarin na gudu. Lokacin da aka sako shi ya shaida wa iyalinmu cewa an daure shi da sarka an sanya masa ankwa kuma aka hana shi abinci. Ya ce ana ba shi abinci sau daya ne ko sau biyu a wuni, kuma galibi ba irin abincin da ya saba ci ba,” inji Koli.
Kyaftin Koli ya ce sakamakon wahalar da ya sha sai kanen nasa ya fara rashin lafiya, “An dauke shi zuwa asibiti, kuma binciken likita ya gano yana da ciwon olsa,” inji shi.
Har wa yau wata takardar kuka da aka tura wa Shugaban Hukumar Kare Hakkin dan Adam ta kasa (NHRC) da Premium Times ta samu kwafenta, lauyoyin iyalin Koli sun ce an daure kanen nasa da sarka hatta a jikin gadon asibitinsa.
Lauyoyin na kamfanin J. Akin Ajayi and Associates, sun ce an tsare kanen Koli a asibitin sojoji da ke barikin Adekunle Fajuyi da ke Ibadan.
Sun ce a matsayinsu na lauyoyin iyalan Koli sun tafi Ibadan tare da wasu iyalansu don gano inda yaron yake da kuma halin da yake ciki.
“A barikin Fajuyi an hana mu ganin yaron duk da nuna musu hotunan yaro da irin dangantakar da ke tsakanin yaron da sojan da yake kula da shi,” inji su.
Duk da cewa an saki Adamu, lauyoyin a takardar kukan da suka rubuta ranar 15 ga Nuwamban bara, sun ce kuskure ne sojoji su huce fushin da suke yi da Kyaftin Koli a kan kanensa.
Ba a samu jin ta bakin Shugaban Hukumar NHRC Mista Chidi Odinkalu, don tabbatar da ko kokarin hukumar ne ya sa aka saki yaron ba.
Kaset din bidiyon da Kyaftin Koli ya sake ya bayyana yadda wasu manyan ’yan Jam’iyyar PDP suka hada kai da hukumomin tsaro domin tafka magudi a zaben Gwamnan Jihar Ekiti. An ji muryoyin manyan ’yan PDP a kaset din suna tattauna dabarun mured zaben Gwamnan, zaben da a karshe PDP ta lashe da gagarumar nasara.
Sai dai wasu daga cikin wadanda ake zargi da suka hada da Musiliu Obanikoro, tsohon Minista a Ma’aikatar Tsaro da Ayo Fayose, wanda ya kayar da Gwamna mai ci, sun musanta kasancewa cikin wadanda suka shirya mured zaben, inda suka nuna shakku kan sahihanci kaset din da aka dauka.
Sai dai Ministan Harkokin ’Yan sanda, Jelili Adesiyan, wanda ya halarci zaman ya tabbatar a ranar Lahadi cewa kaset din sahihi ne, sai dai ya ce ganawar ba a kan shirin magudin zabe na Ekiti ba ne.