…Fallasar baturen Austireliya kan Boko Haram:
Shi kuwatsohon gwamnan Kaduna Kanar Hameed Ali, cewa ya yi, “Ai dama biri ya yi kama da mutum, domin mun dade muna fadin cewa wannnan kashe-kashe da aka yi a yankin Arewa wadansu ne tsiraru a cikinmu ke haddasa shi, amma aka ki daukar mataki a kai. Sai ga shi Allah Ya sa daya daga […]

Shi kuwatsohon gwamnan Kaduna Kanar Hameed Ali, cewa ya yi, “Ai dama biri ya yi kama da mutum, domin mun dade muna fadin cewa wannnan kashe-kashe da aka yi a yankin Arewa wadansu ne tsiraru a cikinmu ke haddasa shi, amma aka ki daukar mataki a kai. Sai ga shi Allah Ya sa daya daga cikin mutanen da su da kansu suka dauko shi domin ya yi masu aiki ya fito fili ya fadi cewa da Ali Madu Sharif da shi Ihejirika ne ke da hannu a wannan kashe-kashen.’’
‘’Saboda haka mu a matsayinmu na wadanda suka dade suna magana a kan abin, mun yarda da abin da baturen ya fadi. Domin ba na tsammanin zai yi masu karya don kawai ya bata masu suna. Duk abin da zai fadi ba zai yarda ya bata sunansa ba, domin ya san yin hakan zai bata masa nasa mutuncin. Dama dai wadansu ne ke ganin wai turawa ne ko kasashen waje ke haddasa fitina a kasar nan, alhali kuwa akwai mugaye a cikin kasar nan.’’
‘’Muna ganin tun da Allah Ya sa har wannan bature ya fadi sunayen wadanda ya ce suna da hannu wajen ingiza wadannan ‘yan tsiraru a kasar nan, abin da kawai ya rage shi ne gwamnati ta yi maza-maza wajen cafke mutanen biyu, sannan a yi bincike mai tsanani a kan abin da baturen ya fadi, idan har aka gano cewa gaskiya ne sai a hukunta su, hukunci mai tsanani, ta hanyar kai su kotu.’’
Ya ci gaba da cewa, ‘’Idan ba a manta ba, dama shi baturen cewa ya yi sai an kama wadannan mutum biyu sannan za a kawo karshen wannan fitina, saboda ta hanyarsu ‘yan ta’addan ke samun abubuwa.’’
Sheriff da Ihejirika ke daukar nauyin Boko Haram – Dabis
Shi dai wannan Baturen na kasar Austireliya Stephen Dabis da ke jagorantar tattaunawa da mayakan Boko Haram domin kubutar da ’yan matan garin Chibok da aka sace a Jihar Borno, ya shaida wa wata kafar talabijin cewa tsohon Gwamnan Jihar Borno Sanata Ali Modu Sheriff da tsohon Babban Hafsan Sojin Najeriya Janar Azubuike Ihejirika a matsayin wadanda ke daukar nauyin mayakan Boko Haram.
A wata hira ta musamman, Dabis ya shaida wa gidan talabijin na Arise News Tb cewa mutanen biyu suna da hannu a ayyukan Boko Haram a Najeriya tare da kira ga gwamnatin Najeriya ta kaddamar da bincike a kai.
A cikin hirar, Dabis ya ce wasu ’yan siyasa a Najeriya suna da hannu dumu-dumu a rikicin na Boko Haram.
Sai dai wasu jaridun Najeriya sun ruwaito tsohon babban hafsan sojin kasar yana musanta zargin.
Jaridar banguard da ake bugawa a Legas ta ruwaito Janar din yana karyata zargin tare da caccakar tsohon Ministan Abuja Nasir El Rufa’i wanda ya fara saka labarin a shafinsa na Facebook.
Janar Ihejirike ya kuma shaida wa jaridar Thisday cewa wannan wani salon ne na karkatar da hankalin duniya da ke kokarin ganin an kawo karshen rikicin Boko Haram a Najeriya.
Amma a cikin tattaunawar Baturen na Austireliya ya bayyana yadda yake tattaunawa da Boko Haram tare da kira ga gwamnatin Najeriya ta cafke Modu Sheriff wanda ya ce tunda dadewa yake daukar nauyin ayyukan Boko Haram.
Rabaran Dabis ya ambaci tsohon shugaban sojin Najeriya wanda ya yi ritaya a watan Janairu a matsayin daya daga cikin masu hannu a rikicin Boko Haram.
Baturen ya bayyana irin tallafin da mayakan Boko Haram ke samu daga ’Yan siyasa a Najeriya da suka hada da tallafin kudi da motoci kirar Hilud.
Dabis ya ce ya yi aiki da shugabannin Najeriya da suka gabata, Musulmi da Kirista amma kuma yanzu yana mamakin yadda abubuwa ke tafiya. A cewarsa babban kalubalen da yake tunanin Shugaba Goodluck Jonathan ke yin fargaba a kai shi ne samun baraka idan har ya fara cafke ’yan siyasa a kan Boko Haram. Ya ce idan ya fara cafke manyan ’yan siyasa, manyan kasashen duniya irin su Faransa da Birtaniya da Amurka za su fara zarginsa a kan yana karya ’yan adawa don ya ci zabe.
Dabis ya ce akwai wadanda suke da hannu wajen sace ’yan matan Chibok amma akwai dubarun da yake bi wajen tattanawa don ganin an kubutar da su.
SAS: Ba na daukar nauyin Boko Haram
Tsohon Gwamnan Jihar Borno Sanata Ali Modu Sheriff, ya musanta zargin cewa yana daga masu daukar nauyin ’yan Boko Haram, inda ya ce ana son bata masa suna ne kawai.
Ya ce wasu mutane ne ke neman shafa masa kashin kaji kawai domin ya sauya sheka zuwa PDP daga APC.
Tsohon Sanatan yana mayar da martani ne ga bayanin da dan kasar Ausitreliya, Stephen Dabis, ya yi cewa wasu kwamandojin Boko Haram ne suka tabbatar masa da hakan.
Ali Shariff, ya ce wasu ne suka biya Baturen domin ya bata masa suna kawai.
Kuma ya ce zai shigar da karar Baturen a Ingila inda ya je ya bayyana wannan kazafi, maimakon tun yana Najeriya ya fada.
Shi dai Mista Dabis, yana shiga tsakanin ’yan Boko Haram ne da gwamnati domin ceto ’yan matan nan ’yan makarantar Chibok da ’yan Boko Haram suka sace.