Fallasar baturen Austireliya kan Boko Haram: Dattawan Arewa sun bukaci a binciki Ihejirika da Modu Sharif
A makon jiya ne wani baturen kasar Austireliya Rabaran Stephen Dabis, da shugaba Jonathan ya gayyato shi domin ya shiga tsakani ‘yan Boko Haram su amince su sako ‘yan matan Sakandaren Chibok da suka yi garkuwa da yau kwanaki 144 ke nan,ya fasa kwai a wata hira da ya yi da wani gidan talabijin na […]

A makon jiya ne wani baturen kasar Austireliya Rabaran Stephen Dabis, da shugaba Jonathan ya gayyato shi domin ya shiga tsakani ‘yan Boko Haram su amince su sako ‘yan matan Sakandaren Chibok da suka yi garkuwa da yau kwanaki 144 ke nan,ya fasa kwai a wata hira da ya yi da wani gidan talabijin na Ingila, inda ya bayyana cewa tsohon shugaban sojojin kasa na Najeriya Ihejirika da tsohon gwamnan jihar Borno Ali Modu Sharif ne suke taimaka wa ‘yan Boko Haram.
A sakamakon wannan zargin da baturen ya yi ne Aminiya ta tuntubi wadansu dattawan Arewa; irin su Farfesa Ango Abdullahi da tsohon gwamnan jihar Kaduna Kanar Hameed Ali da kuma kungiyar kare muradun Arewa (ACF) domin jin ta bakinsu game da wannan tonon sililin da Rabaran Dabis ya yi.
Tun farko mun yi zargin cewa akwai boyayyar manufa -Ango Abdullahi
Aminiya ta tattauna da Farfesa Ango Abdullahi game da tonon sililin da Rabaran Stephen Dabis wani baturen kasar Austireliya ya yi, inda ya bayyana wadansu jiga-jigai a kasar a matsayin masu taimaka wa ‘ya Boko Haram.
Aminiya: Kwanan nan wani baturen kasar Austireliya Rabaran Stephen Dabid wanda shugaba Jonathan ya kira shi domin ya shiga tsakani ‘yan Boko Haram su sako ‘yan matan Chibok ya yi fallasar cewa Ihejerika da Ali Madu Sharif tsohon gwamna jahar Borno ne suke taimaka wa ‘yan Boko Haram. A matsayinka na dadtijon Arewa da kuka taba barazanar maka Ihejerika a kotun duniya, me za ka ce game da tonan sililin da wannan baturen ya yi?
Farfesa Ango: Ku ‘yan jarida idan za ku iya tunawa shekaru biyu ke nan tun lokacin da abin nan yake ta kara tabarbarewa, na yi magana da ku,inda na ce akwai ‘yan Hoko Haram iri uku ne, shekara biyu ke nan. A tunanimmu kuwa wancan lokacin akwai alamar Boko Haram wadda ta wuce ‘yan Boko Haram da Muhammadu Yusuf ya fara masu sanye da tsumma, sai kuma Boko Haram wanda yake ‘yan ta’adda ne na kasa, barayi masu fashi ne da sauransu da suke fasa bankuna da sunan Boko Haram, wanda da an ga barna sai a ce ‘yan Boko Haram ne, ko a wancan lokacin na ce ni ina zargin cewa akwai Boko Haram wadda ta wuce wadannan guda biyun, akwai Boko Haram wadda nake gani kamar tana da alaka da hukuma, shekara biyu ke nan. To kuma a hankali ita gaskiya ko ka yi kokari ka rufe ta sai ta fito. Wannan zargi ba sabo ba ne. Abin da Murtala iyako da ya gaji yana gwamna ya fara magana a kai ke nan, ya ce ya tabbatar akwai wata alaka tsakanin wannan tashin hankalin da ake ta yi da kuma kashe mutane da ake ta yi, da gwamnati a ciki. Saboda wannan ne suka matsa masa har suka yi yadda aka fitar da shi daga gwamna. To saboda haka nan shi wannan baturen ya ce ya zauna da kwamandojin Boko Haram daban-daban a kan yadda za a taimaka a fito da ‘yan matan Chibok da kuma yadda suke ayyukansu, ta nan ya fahimci cewa babu shakka Boko Haram wadda Muhammadu Yusuf ya kafa tare da almajirai masu tsumma ba ita ba ce a kasa, Boko Haram din da su Mohammadu Yusuf suka kafa ko tsuhowar Fijo ba su da ita a lokacin da suka fara. To amma sai ga shi a yau abin da ake gani ta kafafen labarai na wadda shirinsu ya nuna cewa ga alama ‘yan Boko Haram ma suna da kayan aikin da sojojin Najeriyar ma ba su da shi, ta fuskoki da yawa. Ta manyan bindigogi ne, ta motoci ne, a ce ga shi can sun zo da mota (Hilud) dari a yi kaza, a yi kaza, a wuri kaza a tafi, kuma a cikin Sahara sararin Allah ta’ala ana ganin komai, ba wai kurmi ba ne ballantana ma ko a ce ba za a iya ganin abin daga sama ba. Ya ce ana ganin yadda suke jerin gwano na motoci suyi gaba, su yi baya. Kuma mutane sun ga wurare da yawa inda jirage masu saukar ungulu za su aje nan, su aje can. Ina su ’yan Boko Haram na asali za su samu wannan?
Kwananna muke ta jin labarin abin da yake faruwa a Binuwai inda ake zargin Fulani da tada hankali, to shi bafulatani yaushe ya san wani abu bindiga, ko a ina ya ga jirgin sama? wanda Fulani daga sanda sai wuka, sai kuma adda na sarar wa dabbobi abinci. Aka ce an gansu suna zuwa da ma jirage, domin wai su ci kasar Tibi.
Saboda haka wannan duk abu ne a wajanmu da ake ta shiryawa domin a maida mu baya, kuma wannan abun ba yadda za a shirya shi ba tare da sanin wadansu mayan mutane a cikin gwamnati ba. To sai ga shi Allah Ya kawo mu lokacin da za a ce wai shugaban sojojin Najeriya, ka san kuwa shugaban sojoji Najeriya banda shugaban kasa babu wani sai shi, ko yaki ake yi, sai ga shi an ce yana cikin masu taimaka wa wadannan mutane da ake zargni sune ‘yan Boko haram, da kuma wani tsohon gwamna, wanda shi shugaban kasa ya gabatar da shi a wani taro ya ce Ali Madu Sharif abokinsa ne. Kuma kwanan nan muna gani aka rufe filin jirgin sama na Barno, har ma aka hana masu zuwa ummara tashi, amma sai ga shi shi kadai aka bude masa ya shiga, ya fita.
Kuma shi wannan bature Rabaran Stephen Dabis ya ce yana da wadansu sunayen da bai fada ba kuma nan gaba zai fada, amma dai wadannan biyun ya ce zai fara da su, domin sune jiga-jigai na wannan abu, da shi tsohon gwamna wanda abokin wannan gwamnati ne, kowa na gani, kuma ya ce zai bar jam’iyyarsa ya koma jami’yyar abokinsa. Shi kuma shugaba sojojin. Najeriya wanda zai iya yaki saboda ya kare Najeriya, ko da zai mutu ne saboda Najeriya, sai ga shi cikin wanda ake cewa ya bada taimako inda za a kashe nasa sojojin wanda suke fagen fama, kuma an kashe mutane babu iyaka, kuma har yanzu ba a san iyakar wadanda aka kashe ba.
Saboda haka mu warimu yanzu ba ma rasa zargin cewa shi kansa shugaban kasan ba zai ce bai san wannan abu ba, domin dai shi shugaban sojoji nasa ne, kuma an ce da hannunsa a ciki, abokinsa Ali Madu Sharif kuma yana ciki, to soboda haka ya zai ce bai sani ba? Kuma mutanan Arewa manya-manya da ya kamata su ce wani abu, kuma suna cikin gwamnatin sun ki cewa komi.
Aminiya: Kasancewar shi wannan bature shugaban kasa ne ya kira shi domin ya amince masa kuma ga irin furucin da ya yi na fallasa wadannan mutane, wace shawara za ka ba shugaban kasa?
Farfesa Ango: Ba ni da wata shwara da zan ba shi, sai dai ba mu yarda da yadda yake tafiyar da al’amarin ba tun farko, kuma muna zargin cewa yana da wata sha’awa na amfani da wannan tashin-tashina da ake yi na neman dawowa ya ci zabe ta kowace fuska.
Aminiya: Mutanen biyu da aka zarga suna hankoron cewa z asu kai kara koton duniya, me za ka ce?
Farfesa Ango: Ai na ji an ce baturen ya ce a shirye yake, su je su yi karar ya gani, mu kuma ba wai maganar a je kotu ba ne, magana ce kawai ta a hukunta su.
kungiyar ACF
Ita ma kungiyar kare muradun Arewa (ACF) ta yi wani zama a ranar Talatar da ta wuce domin tattauna matsalar tabarbarewar harkar tsaro a kasar nan, musamman a yankin Arewa maso gabas, kamar jihohin Borno da Yobe da Adamawa. A bayanin bayan wannan taron mai dauke da sa hannun jami’an yada labaranta Malam Muhammad Ibrahim, ta ce sun tattaunaa kan zarge-zargen da baturen kasar Australiya Dokta Stephen Dabis ya yi, wanda gwamnati ta dauko domin shiga tsakaninta da ‘yan kungiyar Boko Haram don samun nasarar karbo ‘yan matan nan na Chibok da aka sace a ranar 14 ga Afirilun 2014, wanda ya yi zargin cewa tsohon Gwamnar Borno Sanata Ali Madu Sharif da kuma tsohon Babban hafsan sojojin kasar nan Ihejirika suna da hannu wajen daukar nauyin ‘yan kunkiyar Boko Haram a kasar nan.
Saboda haka kungiyar ACF ta yi kira da babban murya ga gwamnatin tarayya da ta tabbatar ta bincike wannan zargi da baturen ya yi wa Ali madu Sharif da Ihejirika, domin gano gaskiyar lamarin. ‘’Muna son duk wanda aka samu da hannu wajen daukar nauyi ko taimakawa wajen aikata wannan babban laifi a kasar nan a hukunta su, saboda ya zama darasi a nan gaba.
Cigaba a shafi na 3