Fam 100 na ba shata ya yi mini waka – Idi Na Tajo Maisaniya
“Idi Na Tajo Maisaniya Allah Ka maida ni can Apapa domin Na Tajo Mai Saniya. Ka tuna kankanana Shanun Kurmi Idi Na Tajo ba naka ba, Ga shanun shi nan sun danno’ Ba don kai ba da kaguwa za su ci.” Idi na Tajo Maisaniya yana daya daga cikin mutanen da marigayi Alhaji Mamman Shata […]

“Idi Na Tajo Maisaniya
Allah Ka maida ni can Apapa domin Na Tajo Mai Saniya.
Ka tuna kankanana Shanun Kurmi Idi Na Tajo ba naka ba,
Ga shanun shi nan sun danno’
Ba don kai ba da kaguwa za su ci.”
Idi na Tajo Maisaniya yana daya daga cikin mutanen da marigayi Alhaji Mamman Shata Katsina ya yi wa waka a lokacin rayuwarsa. Wakilin Aminiya ya je har garin karaye don ganawa da Malam Idi karaye, wanda shi ne asalin sunan dattijon da aka yi wa wakar. A hirar da Aminiya ta yi da shi, ya ce ya boye sunan garinsu ne, ya bayyana Idi kawai saboda kasancewarsa dan limamin karaye domin kada a ce ya lalace. Kuma da Shata ya tashi wakar maimakon ya hada shi da maigidansa Malam Sada a cikin wakar sai ya ce, Idi Na Tajo.
Wannan dan taliki wanda tsufa ya zo masa kuma ga rashin koshin lafiya, ya bayyana mana yadda suka hadu da Shata da kuma irin kyautar da ya yi masa, har ya wake shi:
Abubakar AbdurRahaman Dodo a karaye
Aminiya: Za mu so jin tarihin rayuwarka, musamman jin yadda ka yi fice a wakar Shata?
Idi Na Tajo Maisaniya: A lokacin da na bar gida, nan karaye ni ne babba a gidan Limamin karaye. Na shiga duniya sama da shekara 50, inda na yi ciniki da Turawa, ina sayar musu da kayan gumaka. Na sayar da kaya a Gboko da Dagema da Bugama da Rugam a Jihar Benuwai, sai kuma a can Kudu, inda na yi wannan sana’a a garuruwan Brass da Sepele da Warri da Ekaro. Kai har bakin Bahar (teku) na je, inda ake cewa iyakar duniya. Na shafe sama da shekara 40 ina wannan sana’a.
Aminiya: Ko za ka bayyana mana yawan shekarunka?
Idi Na Tajo Maisaniya: Shekaruna sun kama daga 86 zuwa 88.
Aminiya: Ko za mu san yawan iyalinka?
Idi Na Tajo Maisaniya:’Ya’ya biyu kawai na haifa a duniya, amma ina da jikokina 12; kowane dana yana da ’ya’ya shida.
Aminiya: To, yaya aka yi ka hadu da Shata har ya yi maka waka?
Idi Na Tajo Maisaniya: Wata rana na sauka a Apapa, shi ne yana yi wa maigidanmu Sada waka, sai na dauki jaka guda irin ta da na ba shi, wato fam 100 ke nan, sai na ji ya rera mini wakar Idi na Tajo Maisaniya, har ya ce:
“Allah Ya kai mu Apapa mu ga Idi Na Tajo Maisaniya,
kananan Shanu ba nashi ba,
Ga shanun shi nan sun danno,
Ba don kai ba da kaguwa za su ci.”
A lokacin ba ni son in fadi suna don kada ’yan uwana su ce na lalace, tunda a lokacin ni ne babba a gidan Limamin karaye. Sunan da aka fi sanina da shi, shi ne, Malam Idi karaye, amma da Shata ya tambayi sunana sai na ce sunana Idi kawai.
Aminiya: Da ma kai kana sana’ar kai shanu ne zuwa Kudu?
Idi Na Tajo Maisaniya: Eh,
Aminiya: To daga ina kake samo su?
Idi Na Tajo Maisaniya: Daga Jamhuriyar Nijar nake sayowa.
Aminiya: Kamar su wane ne da za ka iya tunawa wadanda kuka yi irin wannan sana’ar da su?
Idi Na Tajo Maisaniya: Daga Ijegu dai sai abokaina wadanda suke a Gboko ta Jihar Benuwai suna nan ko sun mutu, oho!
Aminiya: Mene ne sunayensu?
Idi Na Tajo Maisaniya: Akwai Shehu da Ibrahim da Muhammadu su ne abokaina
Aminiya: Wacce daukaka kake ganin wakar Shata ta jawo maka?
Idi Na Tajo Mai saniya: Wacce ta jawo mini, duk duniya ai ana ji, ana sawa
Aminiya: Yanzu yaya za ka kwatanta wakar Shata da ta sauran masu kade-kade da raye-raye na zamani?
Idi Na Tajo Maisaniya: Ni ba zan taba kwatanta Shata da wani mawaki ba, in ban da Shata ban san wani mawaki ba.
Aminiya: Kwanaki an ce mana ka yi jinya, wacce irin larura ke damunka?
Idi Na Tajo Maisaniya: Zazzabi na yi mai zafi, an ce taifod ko maleriya.
Aminiya: Ko za ka iya bayyana mana wani abu na tarihi da ka sani, kamar lokacin yakin Ojukwu?
Idi Na Tajo Maisaniya: Lokacin yakin Ojukwu ina Benin aka yi, sai ya koro mu. Daga nan na koma Benuwai, shi ne na hadu da matata na aureta. Yau shekararmu 46 da ita.
Aminiya: Da an yi maka wata matar ne a gida kafin a tafi can?
Idi Na Tajo: Auren fari a Gusau na fara yin sa. In dai ka je Gusau ka ce Malam Idi karaye, to za a kai ka har gidana.