…Fankama da alfahari suka sa PDP ta fadi a zabe – Lamido
Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido ya ce fankama da alfahari da rashin daukar shawara daga shugabannin Jam’iyyar PDP da kuma matsalar rashin tsaro ne dalilan da suka sa jam’iyyar ta fadi a zabubbukan da suka gabata. Gwamna Sule Lamido ya fadi haka ne a lokacin da ya amshi bakuncin Muhammad Lawal wanda ya yi […]
Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido ya ce fankama da alfahari da rashin daukar shawara daga shugabannin Jam’iyyar PDP da kuma matsalar rashin tsaro ne dalilan da suka sa jam’iyyar ta fadi a zabubbukan da suka gabata.
Gwamna Sule Lamido ya fadi haka ne a lokacin da ya amshi bakuncin Muhammad Lawal wanda ya yi tattaki daga garin Hadeja zuwa Dutse don taya Gwamnan murnar kammala mulki lafiya.
Gwamna Lamido ya ce da a ce jam’iyyarsu ba ta yi fankama da girman kai ta ki daukar shawara ba, da ta magance matsalar rashin tsaro a sassan kasar nan, kuma da ba ta fadi a zaben da ya gabata ba.
Ya soki lamirin mutanen Jigawa masu nadamar faduwar Jam’iyyar PDP a zabe, ya ce mutanen Jigawa ba su da wata hujjar yin nadama. Ya ce duk da faduwarsu a kujerar Gwamna da sauran madafan iko, a matakin jiha da tarayya, Jihar Jigawa ta wuce a yi mata bakin mulki irin na jahilliya domin yanzu kan jama’a ya riga ya waye.
Ya ce, “Jihar Jigawa jiharmu ce, mu taru mut aya wadanda suka yi nasara addu’a mu ba su goyon baya don ganin sun kai jihar wani mataki da muke da bukata ta kai, nan da shekara 15 masu zuwa jihar za ta zama tamkar tauraruwa a Afirka. Jihar Jigawa jiharmu ce, tunda mun fadi a zabe haka Allah Ya so, ba mu da hujjar yin fushi, fushi ba namu ba ne, ba mu da hujjar yin fushi don mun rasa mulki. Don me za mu yi fushi don mun rasa mulki? Bai kamata mu yi fushi ba domin ai mun yi mulkin a baya.”