Fanna Inna Abdulrahman: Shekaru fiye da 30 na shayar da ilimi
Farfesa Fanna Inna Abdulrahman ta yaye masu digirin digirgir fiye da 10
Farfesa Fanna Inna Abdulrahman ta yi shekara fiye da 30 tana karantarwa ko tana shugabanci a jami’a.
A shekarunta na karantarwa a Jami’ar Maiduguri ta sa ido a kan rubutun makalar sauka ta dalibai masu didgiri na farko akalla 275, ta sa masu digiri na biyu sama da 35 a hanya, sannan ta horar da masu digirgir, wato digiri na uku, akalla 15 (biyar daga cikinsu kuma sun zama farfesoshi).
Sannan Bakuwar Mai Tantance Makalar Karshe ce a Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi, da Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya, da Jami’ar Jihar Yobe, da kuma Jami’ar Tarayya ta Gashuwa.
Bugu da kari, Farfesa Fanna ta rubuta makaloli fiye da 150 wadanda aka wallafa a mujallun ilimi na gida da na waje.
A yanzu haka, tauraruwar tamu ce Mataimakiyar Shugaban Jami’ar Jihar Borno a bangaren Mulki; kafin nan kuma malama ce a Jami’ar Maiduguri, inda take karantar da Kimiyyar Harhada Sinadarai.
Dadin dadawa kuma za a iya cewa babu wani mukami na jami’a da ba ta rike ba – watakila sai can kololuwar; amma ko shi a matsayinta na Mataimakiyar Shugaban Jami’a ta taba rikewa.
Ayyukan al’umma
Farfesa Fanna Inna Abdulrahman mamba ce a Kungiyar Masana Harhada Sinadarai ta Najeriya, kuma Shugabar Cibiyar Kwararrun Masu Harhada Sinadarai ta Najeriya.
Baya ga digiri uku da take da su a fannin Harhada Sinadarai, tana kuma da digiri na biyu a fannin Mulki da Gudanarwa.
Watakila ma saboda kwarewarta a harkar Mulki ne ta yi shekera 12 (daga 2000 zuwa 2012) tana shugabantar Sashen Harhada Sinadarai na Jami’ar Maiduguri.
Duk da wadannan ayyuka da take yi, Farfesa Fanna kan samu lokaci ta yi aikin al’umma.