Fara da tururuwa
Wata rana a lokacin bazara fara tana zaune tana shan iska cikin kasala saboda irin koshin da ta yi kasancewar a wancan lokaci rayuwar tana da kyau da inganci. Tana nan zaune sai ta ji motsi a cikin ciyayi sai ta daga ganyayen da ke wurin domin ta ga abin da ke faruwa. Sai ta […]
Wata rana a lokacin bazara fara tana zaune tana shan iska cikin kasala saboda irin koshin da ta yi kasancewar a wancan lokaci rayuwar tana da kyau da inganci. Tana nan zaune sai ta ji motsi a cikin ciyayi sai ta daga ganyayen da ke wurin domin ta ga abin da ke faruwa. Sai ta yi ido biyu da tururuwa sai ta ce mata me kike yi a nan haka? Sai Tururuwa ta ce “Kin gani masara nake tsinta don in kai rumbunmu saboda in yi tanadin gaba?
Sai fara ta kwashe da dariya ta ce ‘Don Allah zo mu yi wasa ko kya hutar da kanki daga wannan wahalar.”
Sai tururuwa ta ce “Gaskiya ba zan iya ba, ina ganin ya kamata rumbunmu ya cika taf saboda lokacin sanyi, ke ma kuma ya kamata ki shirya.”
Sai fara ta kwashe da dariya ta ce “Ni ban damu da zuwan wani lokacin sanyi ba, bayan ga abinci nan baja-baja a ko’ina me zai dame ni?”.
Ita dai tururuwa sai ta yi watsi da maganar fara ta ci gaba da jan masara tana kaiwa rumbunta. Ita kuma fara ta ci gaba da hawa kan ganyaye tana hutawa.
Ana nan sai yanayin sanyi ya zo, kuma ga shi an samu fari (karancin abinci).
Babu abinci ko’ina, duk abincin da aka noma ya kare. Nan fa hankalin fara ya yi matukar tashi saboda an wayi gari ba ta da ko kwayar da za ta sa a bakinta. Can sai ta tuna da tururuwa don haka ta nufi wurinta don ta taimaka mata da abin da za ta sa a bakin salati.
Mu kwana nan.