Fara da tururuwa 2
Da Tururuwa ta ji abin da ke tafe da Fara sai ta ce “kin ga irin abin da nake gaya miki ko, lokacin da nake kokarin tara abincin nan dariya kika rika yi mini kina kallona a matsayin sakarya. To ga irin ta nan. Nan dai Fara ta yi ta ba Tururuwa hakuri sannan Tururuwa […]
Da Tururuwa ta ji abin da ke tafe da Fara sai ta ce “kin ga irin abin da nake gaya miki ko, lokacin da nake kokarin tara abincin nan dariya kika rika yi mini kina kallona a matsayin sakarya. To ga irin ta nan.
Nan dai Fara ta yi ta ba Tururuwa hakuri sannan Tururuwa ta debo mata abinci mai yawa wanda za ta yi amfani da shi na ’yan wasu kwanaki.
Fara ta karva ta yi godiya tare da yin da-na-sanin abin da ta yi a baya.
Darasin labarin:
Yana da kyau mutum ya zama mai tunani a kan abin da zai faru a gaba, kuma ya fahimci cewa ita rayuwa sai ana yi ana tanadi.