Faransa da Rasha sun ci gaba da kai wa IS farmaki
kasar Faransa da Rasha sun ci gaba da yin ruwan bama-bamai a kan yankunan da ke karkashin ikon ’yan kungiyar IS a kasar Siriya.Zuwa lokacin hada wannan rahoton Faransa ta kai hari fiye da sau uku a jere a yankin arewacin kasar.Ministan Tsaron Faransar Jean-Ybes Le Drian, ya ce jiragen yaki guda 10 ne suka […]
kasar Faransa da Rasha sun ci gaba da yin ruwan bama-bamai a kan yankunan da ke karkashin ikon ’yan kungiyar IS a kasar Siriya.
Zuwa lokacin hada wannan rahoton Faransa ta kai hari fiye da sau uku a jere a yankin arewacin kasar.
Ministan Tsaron Faransar Jean-Ybes Le Drian, ya ce jiragen yaki guda 10 ne suka yi wa matattarar ‘yan kungiyar ta IS luguden wuta a birnin Rakka, inda suka kashe akalla mutum 33. An ruwaito cewa galibin mutane sun rasu ne lokacin da aka kai hari kan wasu shingayen bincike da ke titunan birnin.
Wani tsohon mazaunin birnin ya bayyana wa kamfanin dillancin labarai na AP cewa kungiyar ISIS ta karfafa tsaron birnin a zaton da take da shi cewa kungiyar sa-kai ta kurdawa wadda take samun goyon bayan Amurka tana shirin kaddamar mata da hari ta kasa.
Shugaban Rashar bladimir Putin ya ce ya bai wa sojin ruwan kasar da suke a tekun Bahar Rum umarni da su yi aiki tare da sojojin ruwan kasar Faransa.