Faransa ta daina ba da biza a kasashen Nijar, Burkina Faso da Mali

Faransa ta dakatar da duk wasu ayyuka da suka shafi musayar al’adu a tsakaninta da kasashen.

Faransa ta daina ba da biza a kasashen Nijar, Burkina Faso da Mali

Shugaban Kasar Faransa, Emmanuel Macron a Kyiv, babban birnin kasar Ukraine. (Hoto: Sergei SUPINSKY / AFP)

Faransa ta ce ta daina bayar da takardar biza a ofisoshin jakadancinta da ke kasashen Burkina Faso, Mali da kuma Nijar, tare da dakatar da duk wasu ayyuka da suka shafi musayar al’adu a tsakaninta da wadannan kasashe.

Tuni dai wannan mataki ya samu mummunar suka daga kungiyoyi da kuma masu ruwa da tsaki a lamurran da suka shafi yada al’adu daga sassan duniya ba wai a cikin wadannan kasashe uku da abin ya shafa kawai ba.

A cewar wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Wajen Faransa ta fitar, matakin daina bayar da biza da kuma daina musayar al’adu a tsakanin Faransa da kasashen, ya fara aiki ne tun ranar 7 ga wannan wata, to sai dai hakan bai shafi wadanda suka mallaki takardunsu na biza kafin ranar ta 7 ga wata da aka dauki matakin ba.

Tuni Ma’aikatar Harkokin Wajen ta sanar da kungiyoyi daban daban da suka kunshi mutanen da ke da kwarewa a fagen musayar al’adu a cikin Faransa, ta hanyar rubuta musu wasika don sanar da su a hukumance.

A ranar 29 ga wata Yulin da ya gabata ne Faransa ta sanar da dakatar da duk wani taimako da ta ke bai wa Jamhuriyar Nijar, yayin da ta dauki irin wannan mataki kan Burkina Faso a ranar 4 ga watan Agustan da ya gabata.

Alaka tsakanin Burkina, Mali, Nijar da kuma Faransa, ta yi tsami ne sakamakon juyin mulkin da aka yi a kasashen uku da ke yankin Sahel.

An ceto jaririyar da ’yar aikin gida ta sace a Edo

An ceto mutum 58 da aka sace a Kaduna

Sarkin Zazzau ya naɗa sabbin hakimai 7

Hajjin 2025: Maniyyata za su fara ajiye N8.4m a Kaduna