Faransa ta daure masu zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa

Wata kotu a kasar Faransa ta daure wasu mutum uku da ke zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa a birnin Paris.Alkalin kotun ya yanke wa mutanen uku hukuncin da ya kama daga wata shida zuwa goma a gidan yari saboda samunsu da laifin shiga wata zanga-zanga a ranar Lahadi wadda aka shirya don bayyana goyon baya ga  […]

Faransa ta daure masu zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa
Faransa ta daure masu zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa

Wata kotu a kasar Faransa ta daure wasu mutum uku da ke zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa a birnin Paris.
Alkalin kotun ya yanke wa mutanen uku hukuncin da ya kama daga wata shida zuwa goma a gidan yari saboda samunsu da laifin shiga wata zanga-zanga a ranar Lahadi wadda aka shirya don bayyana goyon baya ga  Falasdinawan zirin Gaza.
Mutum na hudu an yanke masa hukuncin je ka, gyara halinka ne; yayin da kuma kotun ta ci tarar wani yaro wanda shi ma aka kama shi da laifin shiga zanga-zangar.
Firaministan Faransa, Manuel balls ya yi Allah-wadai da tashe-tashen hankulan da ya biyo bayan zanga-zangar goyon bayan Falasdinawan a unguwar Sarcelles da ke gefen birnin Paris. Hakazalika, ranar Talata ministocin harkokin wajen tarayyar turai sun yi Allah-wadai da yadda ake ci gaba da samun zanga-zangar kin jinin Yahudawa a kasashen turai. Inda masu zanga-zangar kan kai hari a guraren da suke mallakin Yahudawa ne da kuma guraren ibadarsu. Wanda hakan ya tilasta wa gwamnatin kasar haramta zanga-zanga baki daya.
kasar Faransa ce ta fi kowace kasa a Tarayyar Turai yawan Musulmi da Yahudawa.