Faransa ta roki Morocco kan ta karbi tallafin da ta ke so ta ba ta

Gwamnatin Faransa ta roki kasar Morocco kan ta daure ta karbi tallafin da take yunkurin bata, a dai-dai lokacin da adadin mamata sakamakon girgizar kasa ya zarce dubu 3.

Faransa ta roki Morocco kan ta karbi tallafin da ta ke so ta ba ta

Shugaban Kasar Faransa, Emmanuel Macron

Gwamnatin Faransa ta roki kasar Morocco kan ta daure ta karbi tallafin da take yunkurin bata, a dai-dai lokacin da adadin mamata sakamakon girgizar kasa ya zarce dubu 3.

Macron ya ce ya kamata Morocco ta gane cewa wannan lokaci ne da take bukatar taimako ba wai duba masalahar siyasa ba.

Shugaban kasar Emmanuel Macron ya ce akwai bukatar Morocco ta manta da tsamin alaka da ke tsakaninsu saboda dalili na siyasa ta duba halin da talakawa ke ciki, tare da karbar tallafin da Faransar ke shirin bata.

Ta cikin wani dogon jawabi da ya wallafa a shafin sa na X, Emmanuel Macron ya ce gwamnatinsa na tare da Morocco ko yau ko gobe, kuma a shirye take ta bata tallafi a duk lokacin da ta bukata.

Tun bayan faruwar girgizar kasa ta daren Juma’a, gwamnatin Paris ta ware yuro miliyan biyar da nufin kaiwa kasar Morocco tallafi, sai dai kuma a wani abu mai kama da watsa kasa a ido, Moroccon ta ce ba ta bukatar tallafi daga Faransa.

Alaka dai ta yi tsami a tsakanin Morocco da Faransa tun bayan da ita Faransar ta ke kara kusantar Algeria, kasar da ke makwaftaka da Morocco amma kuma ba a ga maciji.

Haka kuma Moroccon na ganin baiken Faransa kan kin goyon bayan yankin Western Sahara kamar yadda kasashen Amurka da Isra’ila suka yi.

ACF ta yi Allah-wadai da harin Sakkwato, ta nemi a yi bincike

Tinubu ya yaba wa NNPCL kan fara aikin Matatar Warri

Masu son Abba ya tsaya da ƙafarsa za su cuce shi – Kwankwaso

Matatar Warri ta fara aiki bayan shekara 9