Faransa ta yi hayar maguna da za su fafata da beraye
Baya ga Birtaniya gwmanatin Faransa ta yi hayar maguna su shawo kan matsalar beraye. Birnin Paris da ake yi wa lakabi da ‘birnin Haske’ baya ga masoya da ke cin karensu bu babbaka beraye sun addabi birnin. Don shawo kan matsalar beraye, al’amarin da ya addabi dimbin gidaje da gine-ginen gwamanti, Ma’aiaktar Harkokin Wajen kasar […]
Baya ga Birtaniya gwmanatin Faransa ta yi hayar maguna su shawo kan matsalar beraye.
Birnin Paris da ake yi wa lakabi da ‘birnin Haske’ baya ga masoya da ke cin karensu bu babbaka beraye sun addabi birnin. Don shawo kan matsalar beraye, al’amarin da ya addabi dimbin gidaje da gine-ginen gwamanti, Ma’aiaktar Harkokin Wajen kasar ta dauko hayar kyanwowi guda biyu, wato Nomi da Noe don su shawo mata kan matsalar beraye, kamar yadda gidan rediyon Faransa ya ruwaito.
Sauran gine-ginen gwmanati da beraye suka addaba sun hada da Ma’aikatar harkokin cikin gida, tare da ofishin mai magana da yawun gwmanati, Christopher Castaner da ke Rue de Grenelle.
Ma’aiaktar harkokin cikin gida ta ce matsalar bera na da matukar tayar da hankali, musmaman ma abin da aka jiwo daga bakin Sakatariyar ministan Jackueline Gourault, wadda aka ruwaito ta dana tarko “a daukacin ko’ina a dakinta” ofishinta da ke ginin, wanda bai wuce dan taki zuwa fadar Shugaban kasar ta Elysee.
kasar Faransa ba ita ce ta farko da ta dauko hayar maguna ba. Domin a shekarar 2011, wata mage Larrry an kai ta ofishin Firayiministan Birtaniya a gidansa da ke Lamba 10 kan titin Downing don ta kawar da gungun beraye. Kuma ofishin harkokin wajen Birtaniya ma ya taba dauko mage Palmerston, wadda ta’fafata mummunan fada” tare da mage Larrry kan ko wane ne a a unguwar Whitewhall da ke tsakiyar birnin Landan, kamar yadda rahoton ya bayyana a jeridar The Telegraph.
Kyanwowi biyar ne ke da wurin kwana a unguwar Westminster da ke tsakiyar birnin Landan. Nomi da Noe har yanzu ba su bayyana a bainar jama’a ba, amma abin tambaya shi ne ko za su yi karon-batta da junansu, su kwata yadda ta kaya tsakanin Larry da Palmerston.