Faransa za ta dauki sabbin matakai kan ta’addanci
Firaministan Faransa Manuel balls ya sanar da sabbin matakan tsaro sakamakon hare-haren da ‘yan bindiga suka kai birnin Paris kwanakin baya. Harin ya janyo mutuwar mutane 20 wadanda suka hada da maharan su uku. Da yake jawabi a fadar Elysee, Firaministan ya ce za a dauki sabbin ma’aikatan leken asiri fiye da guda 2680 nan […]
Firaministan Faransa Manuel balls ya sanar da sabbin matakan tsaro sakamakon hare-haren da ‘yan bindiga suka kai birnin Paris kwanakin baya. Harin ya janyo mutuwar mutane 20 wadanda suka hada da maharan su uku.
Da yake jawabi a fadar Elysee, Firaministan ya ce za a dauki sabbin ma’aikatan leken asiri fiye da guda 2680 nan da shekara uku masu zuwa, domin bincike a kan masu tsattsaurar akida.
Ya kara da cewa yanzu haka a Faransa fiye da mutane 1300 ake zargi da hannu a kungiyoyin masu jihadi, kuma za a ci gaba da bibiyarsu. Mista ball ya ce gwamnatin Faransa za ta kashe kudi kimanin Dala miliyan 500 domin kare barazanar ta’addanci.
A ranar 7 ga watan nan ne wasu ’yan bindiga suka kai hari ofishin jaridar barkwanci ta Charlie Hebdo da ke birinin Paris, inda mutum 12 ciki har da editan jaridar da kuma wasu ’yan jarida suka rasa rayukansu. Maharan sun ce sun yi hakan ne don daukar fansa bisa zanen batancin da jaridar za yi kan Manzon Allah.