Faransawa sun duro daga gini mafi tsawo a duniya
Wasu hatsabiban Faransa, bince Reffet da Fred Fugen, sun tsallen durowa daga kan ginin duniya mafi tsawo na Burj Khalifa da ke masarautar Dubai, a cikin kasar Hadaddiyar Daular Larabawa. Wannan gini dai an kimanta tsawonsa da mita 828.Wadannan Faransawa biyu, sun bude sabon babi a Kundin abubuwan duniya da suka shahara na Guiness Book […]
Wasu hatsabiban Faransa, bince Reffet da Fred Fugen, sun tsallen durowa daga kan ginin duniya mafi tsawo na Burj Khalifa da ke masarautar Dubai, a cikin kasar Hadaddiyar Daular Larabawa. Wannan gini dai an kimanta tsawonsa da mita 828.
Wadannan Faransawa biyu, sun bude sabon babi a Kundin abubuwan duniya da suka shahara na Guiness Book of Record, a lokacin da suka duro daga Burj Khalifa, a ranar 21 ga Afrilun 2014.
Faransawa dai kwararrun ’yan tsallake ne. don haka a safiyar Litinin din makon da ya gabata, suka fara shiri, a tsakanin karfe shidda zuwa tara na safe suka duro. Rahotanni sun nuna cewa, an taba samun wani dan asalin Hadaddiyar Daular Larabawa, gwanin tsallake, Nasser Al Neyadi da Omar Al Hegelan da suka taba durowa daga wani yanki na ginin, mai tsawon mita 672 a shekarar 2010.
Wasan tsalle da durowa a jikin gine-gine da na’uroprin sadarwa da manyan gadoji, da tsaunuka, wasan kwararru ne da ake yi wa lakabi da “base jumping” a Turancin Ingilishi.
An fitar da hoton bidiyon Reffet da Fugen, inda suka rika yin tsalle da durowa a tsakanin mitoci biyu zuwa uku da ke tulluwar tsinin ginin a daidai lokacin da rana ta fara fiowa. ’Yan wasan tsallen sun yi wannan bajintar ne, lokacin da suke sanye da tufafi masu launin dorawa, wadanda aka cika su da iska, suna kuma aiki tamfar fuka-fukan tsuntsu.
“Muna cike da farin ciki samun shiga kundin tarihin duniya, amma wannan bas hi ne hakikanin abin da muka a sa a gaba ba. Mun dade muna mafarkin durowa daga kan wannan ginin a tsawon shekara uku da suka gabata,” a cewa Fugen dan shekara 34, wanda ya saba yin tsallen badaken mita 600 tun a shekarar 2003, kamar yadda ya bayyana wa jaridar Guldnews.
Wadannan mutane biyu, sun bayyana cewa, sun shafe shekara suna shirin yadda za su bullo wa tsallen durowa kasa daaga kan gini mafi sawo a Dubai. Kuma kungiyar SkyDibe ta Dubai ce ta dauki nauyin shirya tsallen badaken.
A rahoton jaridar Gulfnews, an bayyana cewa, wannan shi ne karo na biyu sd SkyDibe ta shirya tsallen badake da durowa kasa cikin wata guda. A ranar 5 ga Afrilun bana, kwararren dan tsallen badake Ernesto Gainza ya duro da fuka-fukin lema, daga kan ginin mai tsawo da fadin mita 35.