Farashin alkama bai fadi ba – Shugaban Manoman alkama

Alhaji Salim Saleh Muhammad shi ne Shugaban kungiyar Manoman Alkama na kasa. A tattaunawarsu da Aminiya ya musanta batun da ake yin na cewa farashin alakama ya fadi wanda har ya sa manoma fargabar yin shukar alkama a bana, inda ya nuna cewa su a lissafinsu na doka kari ma aka samu a farashin. Ga […]

Farashin alkama bai fadi ba – Shugaban Manoman alkama

Alhaji Salim Saleh Muhammad shi ne Shugaban kungiyar Manoman Alkama na kasa. A tattaunawarsu da Aminiya ya musanta batun da ake yin na cewa farashin alakama ya fadi wanda har ya sa manoma fargabar yin shukar alkama a bana, inda ya nuna cewa su a lissafinsu na doka kari ma aka samu a farashin. Ga yadda hirar ta kasance:

Aminiya: A kwanankin nan manoman alkama na cikin fargaba game  da faduwar farashin alkama. Mesne ne gaskiyar lamarin?

Alhaji Salim: Gaskiyar lamari farashin Alkama ya yi kasa a bangaren kasuwa, akwai tsari guda biyu da ake da shi tsarin da ke a rubuce wato na doka da kuma tsarin yadda kasuwa take tafiya. A tsarin da muka yi na rubutu da doka mu ba za mu ce farashin ya fadi kasa ba, domin kusan kamar kari ma aka samu idan aka kwatanta da bara. A bara mun yi tsarin alkama akan farashin dubu 14 zuwa 15, amma mun dauke shi dubu 18 zuwa 20 kin ga ba faduwa a ciki. Amma idan ka dubi lamari na kasuwa a bara, sai kasuwa ta ba manoman alkama farashi kilo 100 ya kai dubu 35, a bana kuma sai kasuwar ta ba shi dubu 20 zuwa 21. Wannan ya sa ake cewa farashin alkama ya yi kasa. Kuma ita alkama tana da abu guda, yanzu ba mamaki a cikin watan nan da muke na 11 kafin mu shiga wata na 12 za ta iya komawa dubu 30 ko sama da haka, domin yanzu ne lokacin bukatarta. Kin san  lokacin girbi lokaci ne da duk farashin amfanin gona yake faduwa, idan an kwana biyu kuma sai ya tashi. A takaice a tsarin alkaluma na gaskiya mu farashin Alkama bai fadi ba.

Aminiya: A kwanan nan an ji manoman Jihar Bauchi suna kokawa akan ba za su sake noman alkama ba sakamakon rashin kasuwa, me zaka ce akan hakan?

Alhaji Salim: Wannan magana ba manoman alkama ba ne suka fade ta, wani darakta ne daga Ma’aikatar Gona ta Bauchi da muka yi wani taro a wata ma’aikatar fulawa ya yi wannan tsokaci, kan cewa manoma sun noma alkama ba su sami kasuwa ba don haka ba za su sake noma alkama ba. A lokacin bayan ya fadi wannan magana mun nuna masa ba haka abin yake ba, domin abu na farko yanzu da za ki nemi gwammanatinsa ya ba ki kididdiga akan hekta nawa ko ton nawa aka yi a Bauchi, bai sani ba; kawai ya samu dama ne ya zo wajen taro kuma ya yi jawabi na iya abinda ya sani ba tare da tuntubar mu shugabanni na kasa ba. Mu mun san a matsayinmu na shugabanni na kasa mu muke tsara yadda za ayi noman alkama kuma mu fidda tsari na yadda za a sayi alkamar. Mun san an sayi alkama daga Bauchi kamfanin fulawa sun saya sun yi amfani da ita, kin ga ace babu kasuwa ba haka ba ne. Sannan a yanzu haka kusan alkama tafi daraja a Bauchi fiye da Kano, dan yanzu a can farashinta yana Naira dubu 23 zuwa 22, sabanin Kano da yake Naira dubu 20 zuwa 19.

Abin da nake so mutane su fahimta shi ne shi tsari na noma idan ka dauke shi tun daga farko kafin ka fara noma; daga lokacin da ka gyara gonarka har zuwa lokacin girbi sai mun kididdige komai. Idan ka samu wannan kididdiga ka hada shi da abin da ka samu a gonar, ka ba shi farashi na kasuwa a wannan lokacin, to ba manomin da zai ce ya noma alkama ya fadi. Sai dai idan asara ce ta zo masa a gonar wannan fa babu abinda mutum zai iya yi, amma in dai za ka yi ko taku muka samu a hekta daya buhu talatin ke nan, wanda in aka dauke shi akan akalla dubu 15, ya kai dubu 450. Kuma abin da za ka kashe a noman bai wuce dubu 257 ba. Kin ga ba yadda za ayi ace ba riba a harkar alkama. Waccan kasuwar da ta tashi sama ta ba mu Naira dubu 35 hakan ya sa mutane kowa ya shigo noman alkama. Wasu babu ilimin noman wasu ba su san lokacin noman alkama ba wasu kuma ba su da iri mai kyau, saboda haka sai suka ce alkama ma in kayi nomanta ma asara ce. Ban ce noman alkama ba shi da matsaloli ba, yana da su da yawa kuma mun fuskance su da yawa bara.

Aminiya: Ana korafin cewa farashin alkama na gida yana yawa akan farashin wacce ake shigo da ita. Me ya jawo hakan?

Alhaji Salim: Wanann haka ne, amma idan ana so a daidaita farashin sai an yi abu uku. Na farko a samar da iri ingantacce wanda zai baka tan bakwai zuwa tan takwas a hekta daya kamar yadda kasashen duniya suke samu, wasu ma sun wuce haka, domin a Amurka ana samun tan 12 a hekta daya, sannan a samar da injina da za su saukaka noman domin akasarin noma idan kana yi kudin da ake biyan dan kwadago yana fin komai tsada; to idan aka saukaka maka aka samar maka da injina masu sauri kin ga an samu saukin wannan bangare wajen biya. Sannan na uku ya kasance an baka tallafi wato shi ne idan kasuwa ta ki ba da farashi kamar yadda bana ta nuna farashin bai mana kyau kamar na bara ba, to anan sai gwamnati ta shigo ta maye mana wanann gibin.

Idan manomi ya samu wannaan tabbacin na kada ya ji tsoro idan ya yi noma ba zai fadi ba. Za a cicciba shi a tallafa masa. Sannan na karshe ace kuma an samu kasuwarta a kowane lokaci da ka noma da ka samu mai saye shi ke nan noma ta samu. Abin da muke so mutane su gane shi ne ita alkama ba kamar shinkafa ba ce, domin ita shinkafa ana noma ta ne don aci sannan abinda ya rage sai sayar, ita kuma alkama ana noma ta dan a sayar a samu kudi don ba manomin da zai noma alkama buhu talatin ya ce don ya ci, to shekara nawa zai yi bai gama cinyewa ba. Dole kasuwa zai kai ta ya sayar da ita a sarrafa ta ayi fulawa da ita ayi kuma tsakin bura-busko, sannan idan manomin ya dawo ya sayi wannan fulawar sannan ya zo ya sarrafata zuwa gurasa yayi cin-cin ko taliya sannan yakai kasuwa ya sayar.

To kin ga ita alkama ta kowane bangare ana noman ta fiye da shinkafa don neman kudi ne, shi ya sa aka samu ci gaba a noman shinkafa fiye da alkama domin manoman shinkafan nan manoma ne na tali tali ko gwamnati ta tallafa ko kada ta tallafa za su yi nomansu. Ita kuwa alkamar nan sai mu ce kamar bakuwa ce tana nan shekara aru-aru aka watsar da nomanta yanzu kuma aka farfado da ita  wannan karo. Na uku zamu ce  kuma daurin gindinta ya fara daga waccan gwamnatin da ta shude zuwa wannan gwamnatin ta yanzu da ta bunkasa tare da tabbatar da abin ya zauna da gindinsa. A duk shekara Najeriya tana asarar kimanin dala biliyan hudu da miliyan dari biyu akan shigo da alkama. To haka za mu zauna bayan mu muna da kasar muna da ruwan kuma muna da manoman da za su yi noma; abin da muke bukata kawai shi ne abin da na lissafa a baya ingantaccen iri da kananan injina da kuma tabbatar da samun kasuwa tsakaninmu da masu sarrafata, to idan ka samu wannnan za ka iya ciyar da kasar nan abinci.

A yanzu haka duk da kasancewar ba gudunmawar gwamnatin tarayya, babu ingantaccen irin da cibiyar Lake Chad take samarwa, mun noma hekta dubu dari uku a wannan hekta da muka sa alkaluma da mu dauki  mafi karantar abinda muka noma tun da can tan hudu muke sa rai. Idan kika dauki tan hudu a hekta miliyan uku, mun noma tan miliyan daya da dubu dari. Yanzu da aka fara wannan tafiya idan  bana aka inganta mana noman burinmu na bana shi ne mu noma hekta dubu dari biyar wanda in muka tsaya kan alkaluma tan uku a duk hekta, muna da tan miliyan daya da dubu dari biyar. Kin ga an kusan rage rabin abin da ake shigowa da shi daga waje.

Mun san duk abin da Shugaba Buhari ya fada ba wasa yake ba da gaske yake yi kuma abinda yake so ya yi kenan, to amma su mataimakan nasa wajen tabbatuwar wanann al’amari su da gaske suke yi? In da gaske suke yi su dubi wannan kalubale namu su wadata mu da abubuwan da muke bukata. Idan sun ce kule za mu ce cas, nan da lokaci kadan za mu noma alkamar da za ta sa a dena shigo da ita daga waje.

Aminiya: Wane irin tallafi manoman alkama ke samu daga gwamnati?

Alhaji Salim: A bara abin da zai ba ki mamaki shi ne tun daga gwammanatin tarayya har kasa babu wanda ya tallafawa noman alkama. Gwamnati ba ta tallafa mana da kudi ba, ko iri ba ta ba mu injina na amfanin noma ba, akwai cibiyar Lake Chad wanda suke da alhakin samar da irin alkama a bara ko buhu bai samar mana ba, ga kuma bana har yanzu babu wani labari. Ga shi kuma Shugaban kasa Buhari ne ya yi kira da a koma gona domin ya zama wata kafa da gwanati za ta rika samun kudin shiga dan daina dogaro kacokan akan mai. An yarda da wannan tsari an kuma karba amma ba a ba shi kayan da ya kamata ba domin ya bunkasa ba.

Sai kuma matsalar da iri ingantacce a samar da kayan amfanin gona misali ka cire fartanya daga wurin manomi ka kawo masa ‘yan injina kanana da zai yi amfani da su, a kuma samar masa da taki mai kyau. Duk da dai gwamanti na samar da taki mai kyau akan Naira 5,500 kamar yadda gwamnati ta tsara an samu sauki. Amma a tuna wannan taki bangare daya ne kuma shi karan kanshi wannan takin kala biyu muke nema mu yi noma, wannan nikakken ne, akwai inda muke bukatar zuran yuriya wanda shi gwamnatin tarayya ba ta yin sa sai kamfanunnuka, sai dai maonmi ya je ya saya akan Naira 7,500 ko 8000. Kin ga an gudu ba a tsira ba ke nan. To da ace yau za a samu daidaito na wannan farashin sannan a samar da kananan injina na yin noma, manomi ya huta da ciwon baya da ciwon jiki in ya tafi gona, aikin da zai yi a awa uku zai yi shi cikin awa daya ko minti 45, to noma zai bunkasa.