Farashin amfanin gona ya sauka a kasuwannin Taraba 16
Aminiya ta gano cewa a wadannan kasuwannin ne ake samun hatsi a kan farashi mafi sauki a jihar.
Farashin kayan amfanin gona ya sauka a kasuwannin Jihar Taraba, inda jihar ke da manyan kasuwanni tara da ake sayar da hatsi, wanda ake kayan buhu irinsu masara da shinkafa da dawa da gero da gyada da wake.
Sauran kayan amfanin gonar da ake sayarwa sun hada da ridi da agushi, sai kuma kasuwanni bakwai da ake sayar da doya da rogo.
Binciken Aminiya ya nuna cewa wadannan kasuwanni suna ci ne a ranaku daban- daban a kowane mako.
Kasuwanin da ake sayar da hatsi sun hada da kasuwar Mutum Biyu da Tella da Bembel da Sabongida a Karamar Hukumar Gassol.
Sai Kuma kasuwannin Maihula da Garba Chede da Bali da Jatau a Karamar Hukumar Bali.
Sauran kasuwannin kuma sun hada da Iware da Bakin Dutse a Karamar Hukumar Ardo-Kola.
Aminiya ta gano cewa a wadannan kasuwannin ne ake samun hatsi a kan farashi mafi sauki a jihar.
Sai Kuma kasuwannin da ake samun doya a kan farashi mafi sauki da suka hada da kasuwar doya ta Pupule da Hawan Mika da Nyaja da Kassa a Karamar Hukumar Yorro.
Sai kuma kasuwannin Zing da Monkin a Karamar Hukumar Zing inda ake samun doya a kan farashi mafi sauki.
A wadannan kasuwannin masu sayen hatsi da doya daga sassan kasar nan na zuwa domin sayan kayan amfanin gona a kowane mako.
A kasuwannin jihar ne aka fara samun faduwar farashin kayan amfanin a kakar amfanin gona ta bana.
Binciken da Aminiya ta gudanar ya nuna cewa farashin buhun masara ya fadi warwas, inda ake sayar da buhu mai nauyin kilo dari a kan Naira dubu takwas zuwa Naira dubu goma da dari biyar.
Sai buhun shinkafa mai bawo ana sayar da ita a kan Naira dubu goma sha uku zuwa Naira dubu goma sha biyar.
Farashin doya ma a wadannan kasuwannin ya fadi inda doya kwaya daya wacce ke da girma sosai wadda akan sayar a kan Naira dubu daya a watanin baya, yanzu ana sayarwa a kan Naira dari biyar.
Manoma da suka kawo kayan amfanin gonarsu kasuwa domin sayarwa sun nuna damuwarsu kan rashin masu sayan kaya.
Wani manomi wanda ya kawo masara a kasuwar Iware ya shaida wa wakilin Aminiya cewa rashin masu sayan kayan amfanin gona ya haifar da faduwar kayan a jihar.
Wakilin Aminiya ya ga motoci masu yawa ana musu lodin kayan zuwa wasu sassa daban-daban na kasan nan.
Alhaji Abubakar Mafindi, wanda ke hada-hadar sayan kayan amfanin gona ya bayyana cewa a shekarun baya ana samun masu sayan kayan daga jihohin Borno da Kano da Jigawa da Yobe da Bauchi da yankin Kudu maso Gabacin kasar nan zuwa kasuwanin jihar, domin sayan kayan amfanin gona amma a wannan kakar yawan su ya ragu.
Ya ce farashin kayan amfanin gona zai ci gaba da faduwa a jihar saboda nasarar da manoma suka samu a wannan daminar.