Farashin Dala na ci gaba da faɗuwa a kasuwar bayan fage

’Yan canji sun soma fito da Dalar da a baya suka ɓoye a yayin da a yanzu darajarta ke karyewa.

Farashin Dala na ci gaba da faɗuwa a kasuwar bayan fage

A kasuwar bayan fage ta ’yan canjin kuɗaɗen ƙetare a Najeriya, darajar Naira na ci gaba da ƙaruwa a yayin da farashin Dalar Amurka ke sauka.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ’yan canjin ke sayen kowacce Dalar ɗaya a kan N1400 kamar yadda rahotanni suka tabbatar.

Wani binciken da shafin Nairametrics ya gudanar, ya bayyana cewa farashin Dalar na ci gaba da sulalowa ne sakamakon yadda mutanen da a baya suka ɓoye Dalar amma a yanzu suka fito da ita domin sayarwa sakamakon rashin daraja da dalar ke fuskanta.

Sai dai kuma kamar yadda binciken ya nuna, har yanzu ’yan kasuwar na sayar da Dalar a kan N1550 zuwa N1600.

A yayin zantawar jaridar da wani dan kasuwa mai suna Musa, ya bayyana cewa sun yi farin ciki da yadda farashin Dalar ke kara karyewa.

Musa ya bayyana cewa wannan zai ba su damar gudanar da kasuwancinsu cikin kwanciyar hankali.

Sai dai har yanzu ana ci gaba da gudanar da canjin Dalar a kan N1560 a hukumance.

Alakarmu da El-Rufai na nan babu matsala —Uba Sani

Yau Majalisar za ta ci gaba da aiki kan Dokar Haraji

Kotu ta tsige Ohinoyi na Ƙasar Ebira

Kotu ta yanke wa mutum 5 hukuncin rataya a Kano