Farashin danyen mai ya yi warwas bayan ragin da Saudiyya ta yi
Danyen mai ya yi faduwa mafi muni tun rage farashin da Saudiyya ta yi a watan Yuli
Farashin danyan mai ya ragu da Dala daya a kan kowace ganga a ranar Litinin 7 ga watan Satumba, wanda shi ne mafi muni tun rage farashin da kasar Saudiyya ta yi a watan Yulin bana.
Faduwar farashin ya zo ne lokacin da kasar Saudiyya ta yi ragin manta domin jigilarsa zuwa nahiyar Asiya, a cikin watanni biyar baya a lokacin da ake farfadowa daga bukatar man dalilin cutar coronavirus.
- Cire tallafi: Tarihi ba zai manta da Buhari ba —Fadar Aso Rock
- ‘Miliyoyin yara na iya kamuwa da cutar kyanda a Najeriya’
Danyan mai samfurin Brent wanda a baya ake sayarwa a kan Dala 41.75 a kowacce ganga ya fadi da cent 91 kwatankwacin Dala daya a dai-dai 12 na dare, bayan ya ragu da Dala 41.51, a watan Yuli.
Saudiyya wacce ita ce kan gaba wajen fitar da danyan mai a duniya ta bayyana ragin man nata ne na watan Oktoba mai kamawa a hukumance a kan danyan mai samfurin Arab Light wanda ta ke sayarwa ga Nahiyar Asiya.
Kungiyar Kasashe Masu Fitar da Man Fetur (OPEC) da takwarorinta sun saukaka dokar da suka yi ta rage yawan man da kowace kasa take hakowa na ganga miliyan 7.7 a rana a watan Agusta bayan da aka fara farfadowa daga annobar coronavirus.