Farashin fetur na iya tashi bayan Dangote ya daina sayar da mai a Naira

Masana sun yi gargaɗin cewar matuƙar ba a ɗauki matakin gaggawa ba, hakan na iya shafar tattalin arziƙi.

Farashin fetur na iya tashi bayan Dangote ya daina sayar da mai a Naira

’Yan Najeriya na iya fuskantar ƙarin farashin man fetur bayan da Matatar Man Dangote ta bayyana cewa ta daina sayar wa ’yan kasuwa man fetur a kuɗin Naira.

Matatar, wacce ke siyan ɗanyen mai da Naira bisa yarjejeniyar gwamnati, yanzu ta koma sayan ɗanyen mai da dalar Amurka.

An ƙirƙiro yarjejeniyar siyan ɗanyen mai da Naira ne domin rage tsadar mai.

Bisa ga wannan yarjejeniya, Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPCL), yana da alhakin samar wa Matatar Dangote gangar ɗanyen mai a kowace rana 385,000, domin ta tace ta kuma sayar da shi a farashin Naira.

Sai dai rashin cika alƙawari daga NNPCL ya sa yarjejeniyar ta gaza ɗorewa.

Wata majiya ta bayyana cewa, “NNPCL bai cika alƙawarin da ya ɗauka ba, hakan ya sa Dangote ba shi da wani zaɓi illa ya fara siyan ɗanyen mai da dala.

“Yanzu matatun cikin gida sai sun samu dala kafin su iya ci gaba da aiki.”

Matatar Dangote ta ce, “Dole ne mu daidaita kuɗin sayar da kayayyakinmu da kuɗin da muke siyan ɗanyen mai. Yarjejeniyar Naira ba ta samar da isasshen ɗanyen mai da zai iya kula da aikinmu ba.”

Masana sun yi gargaɗi

Masana tattalin arziƙi sun yi gargaɗin cewa wannan mataki zai haddasa tashin farashin man fetur yayin da aka fara samun sauƙin tashin kayan masarufi.

Dokta Thomas Ogungbangbe, wani masanin harkokin makamashi, ya ce, “Idan ana siyan ɗanyen mai da dala, dole ne a sayar da man fetur a farashin kasuwar duniya. Wannan zai ƙara matsin lamba ga dalar Amurka kuma ya jefa ’yan ƙasa cikin ƙarin wahala.”

A cewarsa wannan mataki na iya janyo ƙaruwar shigo da mai daga ƙasashen waje.

“Muna tunanin tace mai a gida zai warware matsalar tsadar mai, amma yanzu muna dawowa kan matsalar da muka nemi mu magance ta,” in ji Dokta Ogungbangbe.

Dokta Marcel Okeke, wani ƙwararre a ɓangaren harkar man fetur, ya buƙaci gwamnati da ta ɗauki matakin gaggawa.

“Dawo da tsarin sayen ɗanyen mai da Naira zai taimaka. Idan ba a yi hakan ba, farashin man fetur zai ƙara hauhawa, wanda zai haddasa tashin gwauron zabin hauhawar farashi kayayyaki da kuma matsi ga tattalin arziƙi,” in ji shi.

Sakamakon tashin farashin canjin dalar Amurka, wasu masana sun yi hasashen cewa farashin man fetur na iya haura Naira 1,000 kan kowace lita a makwanni masu zuwa, idan ba a ɗauki matakin shawo kan lamarin ba.

Ƙungiyoyin ƙwadago sun ja daga

Dangane da wannan lamari, ƙungiyoyin ƙwadago da na kare haƙƙin masu amfani da kayayyaki sun fara shirye-shiryen gudanar da zanga-zanga kan yiwuwar ƙarin farashin mai.

Ƙungiyoyin Ƙwadago na Najeriya na NLC da TUC, sun buƙaci Gwamnatin Tarayya ta ɗauki matakin gaggawa domin daƙile lamarin da ka iya jefa al’umma cikin wahala.

“Wannan mataki da Matatar Dangote ta ɗauka zai sanya rayuwa ta ƙara tsananta ga miliyoyin ‘yan Najeriya da suka riga suka faɗa cikin matsin tattalin arziƙi,” in ji Shugaban NLC, Joe Ajaero.

Farashin kuɗin sufuri na iya tashi

A halin yanzu, ana sa ran hauhawar farashin man fetur zai ƙara tsadar kuɗin sufuri, wanda hakan zai daɗa ta’azzara wahalar rayuwa.

Wasu direbobin mota sun nuna damuwarsu cewa idan farashin mai ya ƙaru, dole ne su ƙara kuɗin abun hawa, wanda zai ƙara dagula halin da talakawan Najeriya ke ciki wajen yin zirga-zirga a kullum.

Idan ba a samu mafita cikin gaggawa ba, tasirin lamarin zai iya shafar tattalin arziƙin Najeriya.