Farashin fetur ya kai N1,080 kan kowace lita a Legas
Yanzu dai farashin man fetur ya fara bambanta a wasu sassan daban-daban na Najeriya.
Farashin Litar Man Fetur ya ƙaru zuwa Naira 1,080 a wasu sassan Jihar Legas, sakamakon tashin ɗanyen mai a kasuwar duniya.
Bincike ya nuna wasu gidajen mai a ranar Asabar sun fara sayar da man tsakanin Naira 1,020 zuwa Naira 1,080 kan kowace lita.
- Iran ta nemi afuwar maƙwabtan ƙasashe ta gindaya sharaɗin daina kai musu hari
- Babu ƙasar da za ta tsoma mana baki wajen naɗa sabon jagora — Iran
Ƙarin farashin ya biyo bayan ƙara kuɗin mai da matatar Dangote ta yi.
Farashin ya shafi masu ɗauko mai kai-tsaye daga matatar mai kafin su sayar wa jama’a.
Rahotanni sun ce matatar ta ƙara farashin zuwa Naira 995 kan kowace lita daga Naira 874, saboda tashin farashin ɗanyen mai a kasuwar duniya.
A yanzu haka ana sayar da gangar ɗanyen mai kusan dala 92.69 kan kowace ganga.
Farashin ɗanyen mai ya ƙaru ne saboda rikicin da ya ɓarke a yankin Gabas ta Tsakiya.
Masana harkar makamashi sun ce rikicin da ya shafi Amurka, Isra’ila da Iran na iya shafar samar da ɗanyen mai a duniya, wanda zai iya ƙara tashin farashin mai.
Masana sun kuma yi gargaɗin cewa idan farashin ɗanyen mai ya ci gaba da ƙaruwa, farashin man fetur a Najeriya na iya tashi har ya kai kusan Naira 1,100 kan kowace lita.
Bincike ya nuna cewa gidajen mai da dama sun riga sun ƙara farashin nasu.
A halin yanzu kuma, rahotanni daga Ibadan sun nuna cewa a wasu wurare ana sayar da man fetur a kan Naira 1,200 kan kowace lita.