Farashin fetur ya sauka bayan tsagaita wuta tsakanin Amurka da Iran
Masana na hasashen cewa farashin na iya ci gaba da sauka bayan cimma yarjejeniyar.
Farashin man fetur ya faɗi ƙasa da dala 95 kan kowace ganga a ranar Laraba, bayan Amurka da Iran sun cimma yarjejeniyar tsagaita wutar wucin gadi.
Farashin man fetur na duniya ya sauka da kusan kashi 13 kimanin dala 94 zuwa dala 95 kan kowace ganga.
- Kisan Filato: An binne mutanen da aka kashe a Jos
- Shinkafa da taliya ba za su sa ka ci zaɓen 2027 ba —Atiku ga Tinubu
Wannan na ɗaya daga cikin manyan sauye-sauyen farashi da aka samu a rana guda a ’yan shekarun baya, bayan makonni da aka shafe ana ana rikici a gabas ta tsakiya.
Faɗuwar farashin ta biyo bayan sanarwar Shugaban Amurka, Donald Trump, na tsagaita wuta na tsawon makonni biyu.
Za a dakatar da ayyukan soji idan aka buɗe buɗe Mashigar Hormuz, hanya mai muhimmanci wajen jigilar man fetur na duniya.
Farashin West Texas Intermediate (WTI), ma’aunin man fetur na Amurka, shi ma ya sauka kimanin dala 95 zuwa 96 kowace ganga, wanda ke nuna cewa rikici a Gabas ta Tsakiya ya ragu, kuma ƙarin kuɗin da ake biya saboda hatsarin rikici ya ragu.
Kafin tsagaita wutar, farashin man fetur ya haura sama da dala 110 kan kowace ganga saboda damuwa game da ƙarancin man fetur sakamakon rikicin.
Yarjejeniyar tsagaita wuta ta dawo da ƙwarin gwiwa cewa safarar man fetur za ta ci gaba, wanda ya sa farashin ya sauka cikin sauri.
Duk da saukar farashin, masana sun yi gargaɗin cewa farashin man fetur har yanzu na canzawa.
A Najeriya, mutane na fatan wannan zai kawo sauƙin farashin mai, wanda ya ninka tun lokacin da rikicin ya fara.