Farashin gangar mai ya kara faduwa zuwa Dala 57

Farashin gangar danyen man fetur a kasuwar duniya ya kara faduwa zuwa Dala 57 duk da cewa ana tsoron yankewarsa a kasuwar saboda ruruwar rikicin kasar Libya.Rahotanni sun bayyana cewa farashin ya fadi kasa da Dala takwas bisa ga yadda aka yi hasashensa cikin kasafin kudin bana ( shekarar 2015) lokacin da  Ministan Kudi Ngozi […]

Farashin gangar mai ya kara faduwa zuwa Dala 57
Farashin gangar mai ya kara faduwa zuwa Dala 57

Farashin gangar danyen man fetur a kasuwar duniya ya kara faduwa zuwa Dala 57 duk da cewa ana tsoron yankewarsa a kasuwar saboda ruruwar rikicin kasar Libya.
Rahotanni sun bayyana cewa farashin ya fadi kasa da Dala takwas bisa ga yadda aka yi hasashensa cikin kasafin kudin bana ( shekarar 2015) lokacin da  Ministan Kudi Ngozi Okonjo-Iweala ta gabatar da kasafin kudin a gaban zauren majalisa. Har ila yau, mako biyu da suka gabata ne tsohon Shugaban Ma’aikatan Farfesa Oladapo  Afolabi a lokacin wani taro a birnin Ibadan , ya bayyana cewa “duk wani hasashen farashin gangar danyen man da za a yi akan abin da ya dara Dala 50 ganganci ne,” inji shi.
Masana sun danganta faduwar farashin da abubuwa da dama da suka hada da: yawansa a kasuwannin duniya da rage sayensa da kasar Amurka ta yi da sauransu. Kodayake, a watan jiya, rikicin tsakanin bangarorin ’yan gwagwarmaya a kasar Libya ya sanya dakatar da fitar da danyen mai daga kasar, wadda a da take fitar da ganga miliyan daya a kowace rana.
Har ila yau, a watan Nuwamba da ya gabata lokacin taron  kungiyar kasashe Masu Arzikin Mai wato (OPEC), an yi tsammanin cewa kungiyar  za ta tilasta wa mambobinta rage hako man, a wani mataki na dakatar da faduwar farashin, amma sai ba ta yi hakan ba, inda ta ce a bar farashin ya daidaita kansa da kansa.