Farashin gas din girki da man jirgin sama ya karye
An samu ragin Naira 300 a kan kilon gas din girki da litar man jirgi, a daidai lokacin da farashin fetur ya yi tashin gwauron zabo a Najeriya
Farashin gas din girki da na man jirgin sama ya fadi da kusan Naira 300 bayan cire tallafin man fetur da gwamnatin Najeriya ta yi.
Aminiya ta gano a wurare daban-daban cewa a ranar Litinin farashin gas din girki ya koma N700 zuwa N800 kowane kilo, sabanin N1,000 da ake sayarwa a makonnin baya.
A ranar Litinin din an cika tukunyar gas mai nauyin kilo 12.5 a kan N6,950 a Jihar Legas, yayin da wasu jihohi ake cikawa a kan N8,000, maimakon N14,000 da ake sayarwa a makonnin baya.
Shi ma farashin litar man jirgin sama ya fado daga kusan Naira 1,000, inda ya koma Naira 620 a Legas; a Abuja kuma N660, sai Kano N680.
- Kasashen da suka rage a Gasar Kofin Duniya ta ’yan kasa da shekaru 20
- Yemi Mobolade: Dan Najeriya ya zama Magajin Gari a Amurka
“Game da man jirgin sama duk da tsadarsa, mutane na ci gaba da yin tafiye-tafiye. Amma bana jin yana da alaka da cire tallafin mai.”
“Farashin na ci gaba da karyewa kuma ba zan iya cewa ga dalili ba, amma ba zai wuce yanayin kasuwa ba ne.
“Wannan ya samo asali ne tun satin da aka cire tallafin mai. Da alama wannan wani yanayi ne na kasuwar man,” in ji wani ma’aikaci.
Amma wani kwararre kan harkokin makamashi, Olusesan Okunade a zantawarsa da Aminiya, ya ce babu alaka tsakanin faduwar farashin gas din girki da man jiragen sama.
Ya ce, “Ina ganin yanayin bukata ne ya sauya; domin a iyakar sanina, babu wani abu da yake da alaka da karyewar farashin.
Shi kuma wani ma’aikaci da ya zanta da Aminiya, ya ce, rage farashin man zai kawo sauki ga harkar sufurin jiragen sama.
Amma da yake karin haske kan lamarin, wani mai sharhi kan tattalin arziki, Mista Babatunde Adeniji, ya ce hakan ba zai rasa nasaba da yanayin ciniki ba.
Ya kara da cewa, “Wani lokaci kayan da mutane suka saya ya kan dauki lokaci kafin ya zo. Don haka da yawa suna samun kayansu a lokuta daban-daban.”
Aminiya ta ruwaito cewa a bara ne farashin man jirgi ya yi tashin gwauron zabi zuwa kusan Naira 1,000 a kowace lita, lokacin da aka shiga kangin matsalar mai, bayan shigo da gurbataccen mai a Najeriya.