‘Farashin gas din girki zai iya tashi a Najeriya mako mai zuwa’
Hakan dai na da alaka da faduwar darajar Naira
Kungiyar Masu Sayar da Gas din Girki ta Najeriya (NALPGAM), ta ce ci gaba da faduwar darajar Naira na iya sa farashin gas ya tashi a Najeriya nan da mako mai zuwa.
Shugaban kungiyar na kasa, Olatunbosun Oladapo, ne ya yi gargadin ranar Alhamis, yayi tattaunawarsa da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya a Legas.
- ECOWAS ta umarci dakarunta su dauki matakin soji a kan Nijar
- Bankin Duniya ya hana Uganda bashi saboda kin amincewa da auren jinsi daya
Ya ce a ’yan kwanakin nan, manyan dillalan gas din sun bayyana cewa farashinsa ya karu, inda ya alakanta hakan da faduwar darajar Naira.
Oladapo ya kuma ce karuwar farashin gas din a kasuwar duniya da karin haraji da karancin canjin kudi da kuma karya darajar Naira na daga cikin dalilan da za su sa farashin ya karu.
“Akwai yuwuwar ya tashi nan da mako mai zuwa saboda farashinsa ya tashi a kasuwar duniya. Dukkan dillalai da masu sayarwa kadan-kadan da kuma ’yan sari duk yanzu suna fama da kalubale.
“Wannan karin farashin abin takaici ne kuma ba da son ranmu za a yi shi ba, ya kamata gwamnati ta taimaka wajen bayar da tallafi ga jama’a domin rage radadi da kuma rage haraji.
“Yanzu alal misali, kowanne kilogiram daya na gas da aka sayar a kan N700, haraji zai kwashi N3.50. Nawa ke nan ya saura a ciki?,” in ji shi.
(NAN)