Farashin gwanjo ya yi tashin gwauron zabo saboda shigowar sanyi

Sakamakon shigowar sanyi, farashin kayayyakin sawa na gwanjo, kamar  suwaita da jaket da huluna da wanduna,  sun yi tashin gwauron zabo a garin Jos fadar Jihar Filato. Binciken da Aminiya ta gudanar a kasuwar kayan gwanjo da ke babbar kasuwar Taminus a garin Jos, ta gano cewa farashin kayayyakin sun tashi sama sosai. Da yake […]

Farashin gwanjo ya yi tashin gwauron zabo saboda shigowar sanyi

Sakamakon shigowar sanyi, farashin kayayyakin sawa na gwanjo, kamar  suwaita da jaket da huluna da wanduna,  sun yi tashin gwauron zabo a garin Jos fadar Jihar Filato.

Binciken da Aminiya ta gudanar a kasuwar kayan gwanjo da ke babbar kasuwar Taminus a garin Jos, ta gano cewa farashin kayayyakin sun tashi sama sosai.

Da yake zantawa da Aminiya kan wannan al’amari, Mataimakin Shugaban ’Yan Kasuwar Gwanjo na Mista Bigs a Kasuwar Taminus, Alhaji Mustafa Lawal ya ce duk da yanayin da kasar nan take ciki, na rashin kudi.  Farashin kayayyakin sanyi na gwanjo, sun yi tsada sakamakon shigowar lokacin sanyi.

Shi ma da yake zantawa da Aminiya wani mai sayar da gwanjo a kasuwar ’yan gwanjon, Malam Iliya Maichibi, ya ce farashin gwanjon ya tashi sama ne saboda yadda jama’a suke bukatarsu, sakamakon shigowar sanyi.

Wani mai sayar da gwanjon Mista Amos Chigozie, cewa ya yi tun daga shigowar wannan wata da muke ciki, mutane suke ta rububin zuwa kasuwar domin sayen gwanjon sakamakon shigowar yanayin sanyi. Don haka farashin kayayyakin suka tashi sama.

Shi ma wani dan kasuwar Malam Hassan Shu’aibu cewa ya yi ganin yadda jama’a suke rububin sayen kayayyakin sanyin, ya sanya manyan dillalan da suke sayar da gwanjon suka kara farashin kayayyakin.

Amma a zantawarsa da Aminiya wani mai sayar da gwanjo, Malam Abdullahi Usman, cewa ya yi farashin gwanjon sun tashi ne sakamakon rufe kan iyakokin kasar nan da gwamnati ta yi.

Ya ce dilar gwanjon da ake sayarwa  a da kafin a rufe kan iyaka a  kan Naira dubu 150, yanzu da aka rufe kan iyakar, ana sayar da ita ce a kan Naira dubu 200.

Wani da ya zo sayen gwanjo mai suna Mista Ebute Destiny, ya koka kan tashin farashin gwanjon, ya ce tashin farashin gwanjon rashin adalci ne.

Ita ma Misis Peace Bitrus da ta zo kasuwar sayen gwanjon, ta yi Allah wadai da tashin farashin kayayyakin. Ta ce ’yan kasuwar sun yi amfani da wannan yanayin ne na sanyi,  suka kara farashin kayayyakin gwanjon.