Farashin kaya ya yi tashin gwauron zabo bayan cire tallafin mai
An ninka farashin wasu kayan masarufi da na sufuri sakamakon tsadar mai bayan cire tallafi
’Yan Najeriya na korafi kan tashin gwauron zabon farashin kayan masarufi da na sufuri bayan janye tallafin mai da ya haddasa tsadar fetur.
Fasinjoji da masu cefane na kokawa cewa tsadar ta kai ga ninka farashin wasu kayayyaki da na kudin mota, sakamakon tsadar man da kuma karancinsa.
Wani mai Babur din kai sako a Kasuwar Kantin Kwari a Kano ya ce, “mun ninka farashi daga Naira 500 zuwa N1,000 saboda tsadar man da za mu sha domin kai wa abokan huldarmu kaya.”
Aminiya ta ruwaito cewa sanarwar sabon shugaban kasa Bola Tinubu na janje ya biyan tallafin mai haddasa karancin man fetur da kuma tsadarsa, inda wasu gidajen mai suke sayar da lita a kan Naira 700.
- Kano: Gwamna Abba ya nada sabon Akanta-Janar
- Yadda hukumomin gwamnati suka salwantar da tiriliyan 3.8 a mulkin Buhari —Rahoto
Hakan ya haddasa tashin gwauron zabon kayayyaki, da na sufuri.
Aminiya ta gano cewa an kara kudin motar Abuja zuwa Kano daga N5,500 zuwa N7,000.
Zariya zuwa Kano kuma ya tashi zuwa N2,000 daga N1,500.
A garin Ibadan na Jihar Oyo, farashin kwanon garin rogo ya karu daga N350 a ranar Litinin zuwa N370 a babbar Kasuwar Bodija market. Garin amala kuma daga N300 ya koma N350.
A ranar Laraba kamfanin Mai na Kasa (NNPCL) sa kara farashinsa na litar fetur daga N197 zuwa Naira 557 a wasu jihohi.
Wani jerin farashin da ya karade gari ya nuna NNPC ya umarci gidajen mansa su rika sayar da lita a kan Naira 557 a Maiduguri, Jihar Borno da kuma Borno da kuma Damaturu, Jihar Yobe, saura jihohin Arewa maso Gabas kuna a kan N550.
A Birnin Kebbi na Jihar Kebbi a yankin Arewa maso Yammaci, lita ya koma N545, a yankin Arewa ta Tsakiya kuma lita N537, in banda a Ilorin da za a sayar N515. A Kudu maso Gabas kuma matsakaicin farashin shi ne N520.
Amma a Uyo, Akwa Ibom da Yenagoa, farashin N515 ne.
N511 ne sabon farashin lita a Kudu maso Kudu; N500 a Kudu maso Yamma, amm Legas kuma N488.
Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) dai ta yi watsi da karin farashin na NNPC, a matsayin kama-karya.
Hakazalika an tashi zaman baram-baram a zaman da gwamnati ta kira kungiyar don tattaunawa kan janye tallafin man da ya janyo ce-ce-ku-ce.
Tuni dai gidajen mai a fadin Najeriya suka kara farashi, ga kuma dogayen layin ababen hawa da ke neman sha.
Wani masanin tattalin arziki ya bayyana cewa cire tallafin man shi ne abin da ya kamata, amma kada gwamnati ta yi sakacin da dillalan man za su rika cin karensu babu babbaka wajen tatsar ’yan kasa ta hanyar tsawwala farashi a duk lokacin da suka ga dama.