Farashin kayan abinci da sufuri ya karu a Taraba

Kwana daya kacal da kara farashin man fetur ’yan kasuwa sun kara farashin kayan abinci na da sufuri a Jihar Taraba.

Farashin kayan abinci da sufuri ya karu a Taraba

Yadda ake hada-hada a wata kasuwa a Najeriya.

Kwana daya kacal da kara farashin man fetur ’yan kasuwa sun kara farashin kayan abinci na da ababen surufi a Jihar Taraba.

Kafin a kara kudin man fetur ranar Talata an sayar da kwanon shinkafa ’yar gida N3,100, amma farashin ya koma N3,400.

Sai kuma masara da doya da wake wadanda su ma aka kara.

Masu babur mai kafa uku da masu motocin haya su ma sun kara kudin haya a kan hanyoyin garin Jalingo da sauran sassarn jihar.

Masu gidajen man fetur suna sayar da Lita daya na man fetur akan kudi Naira dubu daya da Naira Dari.

Binciken wakilin Aminiya ya nuna cewa masu sayar da man fetur ta bayan fage na sayar da Lita daya na man fetur akan kudi Naira dubu daya da Naira Dari uku.

Wasu mazauna garin Jalingo da aka zanta da su sun nuna rashin jin dadinsu kan karin farashin man fetur da Gwamnatin Tarayya ta yi.

Dauda Adamu, maiakacin gwamnatin Jihar Taraba, ya ce, “da ma kafin farashin man fetur jama’a na fuskantar tsadar rayuwa.

“Karin farashin man fetur da aka yi jiya zai kara wa talakawa matsatsin rayuwa.”

Ya nemi Gwaamnatin Tarayya ta janye wannan karin in dai tana da tausayin al’umma.

Gwamnatin Yobe ta tallafa wa magidanta 53,000 da N3.91bn a 2024

Uwargidan Sanata Goje ta tallafa wa mata da matasa a Gombe

An kama bokaye 2 kan zargin yi wa shugaban Zambiya asiri

Kirsimeti: FRSC ta aike jami’ai 1,539 zuwa Kano