Farashin kayan abinci ya ƙara tashi a Taraba

Farashin ya sake tashi duk da yawan amfanin gona da manoma suka samu a jihar.

Farashin kayan abinci ya ƙara tashi a Taraba

Farashin kayan abinci ya sake tashi a Jihar Taraba, duk da nasarar da manoma suka samu na amfanin gona mai yawa.

Binciken Aminiya ya nuna cewa manoma sun samu kaka mai kyau, inda suka samu .asara da riɗi da gyada da doya da rogo masu yawa.

A ‘yan kwanakin nan farashin kayan abinci ya fara sauka, amma kwatsam sai murna ta koma ciki domin farashin kayan abinci ya sake tashi.

Ƙwaruwar masu sayen kayan abinci ne ya haifar da tashin farashin kayan amfanin gona a jihar.

A kasuwanin jihar kayan amfanin gona da ke Iware da Mutum Biyu da Maihula da Serti da Garba-Chede ɗaruruwan masu sayen kayan amfanin gona ne suka shigo suke sayan kayan abinci mai yawa wanda hakan ya haifar da tashin farashin.

A baya ana sayar da buhun masara mai nauyin kilo 100 a kan kudi Naira 38,000 zuwa Naira 40,000.

Amma a yanzu farashin ya ƙaru zuwa Naira 45,000.

Kazalika, ƙarin farashin ya shafi kayan abinci irin su doya da gyada da rogo kamar yadda binciken ya nuna.

Rikicin Masarautar Kano: Tsagin Aminu Ado Bayero zai ɗaukaka ƙara

Yadda Jimmy Carter ya ceto rayuwata – Obasanjo

Sojoji sun lalata sansanin Bello Turji, sun kuɓutar da mutum 7

Wani mutum ya rasu yayin gyaran rijiya a Kano