Farashin kayan abinci ya faɗi warwas a Neja

Manoman da ’yan kasuwa sun bayyana cewa faɗuwar farashi na barazana ga rayuwarsu duk da cewa ’yan Najeriya sun bayyana farin cikinsu game da hakan

Farashin kayan abinci ya faɗi warwas a Neja

Wata kasuwar hatsi (tsohuwar ajiya).

Manoma suna kokawa kan yadda farashin kayan abinci, musamman hatsi yake ta sauka babu ƙaƙƙautawa a Jihar Neja.

Manoma sun bayyana cewa farashin kayan abinci yana ga sauka ne bayan kamfanonin Najeriya sun koma sayowa daga ƙasashen ƙetare.

Manoman da ’yan kasuwa sun bayyana cewa faɗuwar farashi na barazana ga rayuwarsu duk da cewa ’yan Najeriya sun bayyana farin cikinsu game da faɗuwar farashin kayan.

Hassan Ango Abdullahi, Shugaban Ƙungiyar Amana Farmers and Grains Suppliers of Nigeria, reshen Shiroro ya tabbatar wa wakilin Aminiya cewa farashin kayan ya faɗi warwas a wasu manyan kasuwannin jihar.

Ya bayyana cewa kamfanoni yanzu sun fi son sayen kaya daga ƙasashen Chadi da Ghana da wasu ƙasashe saboda farashin can ya fi arha.

Ya ƙara da cewa sun sayi buhun wake mai nauyin kilomita 100 a kan N103,000 da waken soya a kan N105,000 a lokacin da aka fara roro, amma yanzu farashin ya faɗi zuwa N80,000.