Farashin kayan abinci ya yi tashin gwauron zabo

Galibi, akan fuskanci matsalar tashin farashin kayayyaki a lokacin bukukuwa.

Farashin kayan abinci ya yi tashin gwauron zabo

Farashin kayan masarufi ya yi tashin gwauron zabo a sassan Najeriya da kashi 24 cikin 100 a watan Nuwamba.

Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ce ta fitar da alkaluman da ke alamta cewa ’yan Najeriya za su yi bukuwan karshen shekara na Kirsimeti da Sabuwar Shekara cikin yanayi na tsadar kayan abinci.

Hukumar ta ce farashin kayan abincin ya cilla sama ne saboda tashin farashin kayayyaki kamar burodi da man girki da doya da sauransu.

Ta bayyana cewa farashin kayan abinci a Nuwamban 2022 ya karu da kashi 6.92 cikin 100 idan aka kwatanta da Nuwambar 2021.

Ta kara da cewa, tashin farashin kayayyakin da ake fuskanta wata-wata na faruwa ne sakamakon karuwar bukatun jama’a kamar yadda aka saba gani a lokutan bukukuwa.

Ta ce tsadar ta fi kamari ne a bangaren makamashin gas da fetur da kayan mota, kudin motar haya da da sauransu.