Farashin kayan gona ya fadi a Jihar Katsina
Farashin kayan gona, musamman masara da dawa da wake yana ci gaba da sauka a karon farko cikin watanni, a kasuwannin Katsina in aka danganta da yadda farashin yake a sauran jihohi. Kamar yadda jaridar Aminiya ta gano. Kamar dai yadda aka saba farashin hatsi da kayan gona yakan tashi bayan kakarsa ta wuce, musamman […]
Farashin kayan gona, musamman masara da dawa da wake yana ci gaba da sauka a karon farko cikin watanni, a kasuwannin Katsina in aka danganta da yadda farashin yake a sauran jihohi. Kamar yadda jaridar Aminiya ta gano.
Kamar dai yadda aka saba farashin hatsi da kayan gona yakan tashi bayan kakarsa ta wuce, musamman a cikin watan Maris da Afrilu har zuwa watan Mayu.
Wani dan kasuwa mai sayen hatsi a Kasuwar Kafur, Malam Usman Abdullahi, ya ce kamar yadda aka sani yankin Funtuwa a Jihar Katsina ne jagaba wajen noman masara, kuma wannan yanki ya rike wannan kambi ta hanyar tabbatar da cewa ya samar da isasshiyar masarar da ake bukata a kowace shekara.
Ya ce, a duk fadin Arewa maso Yamma, Kaduna ce kadai ta fi yankin Funtuwa noman masara. Wannan shi ne dalilin da ya sanya farashin masarar yake da sauki, idan aka kwatanta shi da sauran sassan kasar nan. “A yanzu ana sayar da buhu Naira dubu 8 ne a nan. Amma, a cikin birnin Katsina ko Mai’aduwa ko Chiranci wadanda duk a cikin jihar nan suke ana sayar da shi fiye da Naira dubu 9,” inji shi.
Ya kara cewa a wannan shekarar, an samu albarkar noman masara da dawa da shinkafa da wake. A cewarsa “Kowace shekara manoma suna mayar da hankalinsu ne ga noma wani nau’in kayan gona ta yin la’akari da farashinsa da irin yadda ake bukatarsa a kasuwa. Musamman kuma ta yin la’akari da yalwar taki da sauran kayan inganta noma. An noma masara da dawa da shinkafa da yawa a bana. Kuma Allah cikin rahamarSa, an samu albarka. Don haka ya sanya ake samunsu a farashi mai rahusa a nan idan aka kwatanta da sauran wurare.”
Da yake magana, wani falken wake a Kasuwar Bakori, Sani Abdullahi, ya danganta faduwar farashin kan yadda aka rungumi noman wadannan kayayyakin gonar gadan-gadan a wannan yanki.
Abdullahi ya ci gaba da cewa manyan kasuwannin hatsi na Kafur da Bakori da kuma Dandume duk suna ta wannan yanki ne, kuma ranakun cin kasuwanninsu, kwanaki biyar na kowane mako. Amma duk da haka manoma na cika wadannan kasuwanni, da irin hatsin da masaya suke bukata.
Abdullahi ya kara da cewa, akasarin kasuwannin da suke sayar da hatsin akan farashi mai yawa sun yi sarin hatsin ne daga kasuwannin birnin Katsina. “haka kuma fatake na zuwa daga Abuja, Sakkwato da Benuwai su je su sayar da tsada a kasuwanninsu.”
Kamar yadda wakilinmu Abubakar Muhammad ya kalato a baya mafi yawan masu sayen masara kamfanoni ne masu yin abincin kaji wadanda, a halin yanzu suka sake dabara suke noma masarar da kansu domin rage kudaden da suke kashewa.
Muhammad yace “tun a kakar shekarar 2017, lokacin da farashin masara ya yi sama, abinda ya haddasa rubanyar kudin da ake kashewa wajen yin abincin kaji, wanda haka ya tilasta ma kamfanoni masu yin abincin suka fara noma masarar da kansu, don rage kudaden da suke kashewa wajen samar da abincin. Hakan kuma ya sanya farashin hatsin ya sauka ainun.”
Kamar yadda Jaridar Daily Trust ta gano a Katsina, buhun masara mai nauyin Kilogiram 100, farashinsa ya kai tsakanin Naira dubu 7,500 zuwa dubu 8,500. Ya danganta da irin nagartar masarar. Amma a Abuja da Binuwai ana sayar da shi daga Naira dubu 12 zuwa dubu 14. Dawa kuwa ana sayar da buhunta daga Naira dubu 13 zuwa dubu 14, a kasuwannin Abuja da Binuwai, amma kuma a kasuwannin Katsina ana sayar da ita Naira dubu 8. Farashin wake kuwa ya sauka daga Naira dubu 20 zuwa dubu 14 ko dubu 17.