…Farashin kayan masarufi ya tsawwala a Yobe
Farashin kayan masarufi ya yi matukar tsawwala a Damaturu fadar Jihar Yobe, sakamakon karuwar bukatarsu a cikin wannan wata na azumin Ramadan. Lokacin da Aminiya ta ziyarci kasuwar kayan abinci a babbar kasuwar Damaturu ta tarar farashin buhun dankalin Turawa ya kai Naira dubu 24 maimakon Naira dubu takwas da aka san shi a baya […]
Farashin kayan masarufi ya yi matukar tsawwala a Damaturu fadar Jihar Yobe, sakamakon karuwar bukatarsu a cikin wannan wata na azumin Ramadan.
Lokacin da Aminiya ta ziyarci kasuwar kayan abinci a babbar kasuwar Damaturu ta tarar farashin buhun dankalin Turawa ya kai Naira dubu 24 maimakon Naira dubu takwas da aka san shi a baya yayin da matsakaiciyar doya farashinta ya kai Naira 500 maimakon Naira 250 kafin Ramadan.
A bangaren kayan miya kuma kwando daya na tumatir ya haura Naira dubu 15 maimakon Naira dubu bakwai, ya yin da buhun tarugu ya haura Naira dubu 23 maimakon Naira takwas.
Da Aminiya ta tambayi Malam Bala Mai kayan miya kan abin da ya haifar da tsawwalar farashin kayayyakin, ya ce lamarin ne ya zo da haka domin dankali da doya duk lokacin da azumi ya zo bukatarsu kan karu, sannan a bana an shiga azumin ne a lokacin karancinsu.
Alaramma Abdulrazak Ya’u mai kayan miya ya ce su kansu masu sayar da kayan, lamarin na ba su mamaki, duk da cewa akan samu irin hakan saboda tumatur din rani ya kare na damina kuma da saura.