Farashin kayayyaki ya ragu karon farko cikin watanni 19 a Nijeriya

Sai dai kuma farashin makamashi na ci gaba da hauhawa a cikin shekara ɗaya.

Farashin kayayyaki ya ragu karon farko cikin watanni 19 a Nijeriya

Hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya sauka a karon farko cikin watanni 19 a cewar mahukunta a kasar.

Hukumar Kididdiga ta Nijeriya (NBS) ta ce a cikin watan Yulin shekarar 2024, hauhawar farashin kayayyaki ya sauka zuwa kashi 33.40%.

Cikin sabbin alkaluman NBS ta fitar a ranar Alhamis, ta ce an samu raguwar tsadar farashin kayayyakin ne da kashi 33.4 cikin 100 a watan Yuli inda aka kwatanta da kashi 34.19 cikin 100 a watan Yunin shekarar da muke ciki.

Hakan na nufin hauhawar ta ragu da maki 0.8% idan aka kwatanta da makin hauhawar a watan Yunin shekarar 2024.

Daga cikin muhimman kayayyakin da farashin nasu ya sauka sun haɗa da shinkafa da masara da ƙwai da burodi da man fetur.

To sai dai kuma farashin makamashi na ci gaba da hauhawa a cikin shekara ɗaya da ta wuce a cewar hukumar.

Daga cikin kayayyakin da hauhawar farashin ta shafa a tsawon shekara guda a kasar sun hada da garin tuwo na samobita, garin doya, fulawa, burodi, hatsi, doya, dankalin turawa, man gyada, man ja, da kayan hada shayi.

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos

Kasuwar Laranto da ke Jos ta yi gobara